Zakkar fidda kai Kudi ko Abinci? – Sheikh Muhammad Bin Uthman Kano

Danna nan domin shiga karatu Online

Maqala

Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah جل جلاله Tsira da Aminci su ƙara tabbata ga Shugban halitta gaba ɗaya, Annabi Muhammd (SAW) tare da iyalan gidanshi tsarkaka da kuma sahabbanshi gwaraza da kuma waɗanda suka bi turbarsu bisa kyautatawa har zuwa ranar ƙarshe.
Bayan haka, hadisan Annabi (SAW) ingantattu ƙarara sun yi umarni da fidda zakkar kono- wato fidda kai-daga abinci ne ba daga kuɗi ba
Daga cikin ire-iren waɗannan hadisan akwai:

1-
عن أبي سعيدٍ الخُدريِّ رَضِيَ اللهُ عنه، قال: ((كنَّا نُخرِجُ في عهدِ رَسولِ الله صلَّى الله عليه
وسلَّم يومَ الفِطرِ صاعًا من طعامٍ….


Fassara:
Abuu Sa’iid al-Khudry (RA) yana vewa:
“MUN KASANCE MUNA BADA SA’I NA ABINCI NE A MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI A ZAMANIN MANZON ALLAH(SAW)

-Albukhary (1510) da kuma Muslim (986)

2-
عن ابنِ عبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عنهما قال: ((فرَض
رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلَّم زكاةَ الفِطرِ؛ طُهرةً للصَّائِمِ مِنَ اللَّغو والرَّفَث، وطُعمةً للمساكينِ؛ مَن أدَّاها قبل الصَّلاةِ فهي زكاة مقبولة، ومَن أدَّاها بعد الصَّلاةِ فهي صدقةٌ مِنَ الصَّدَقاتِ:

Fassara: An samo daga ‘Abdullahi Ɗan ‘Abbaas(RA) yana cewa:

“Manzon Allah(SAW) ya farlanta zakkar fidda kai a matsayin tsarkakewa ga mai azumi daga wargi da kuma ƙazantar harshe kuma a matsayin ABINCI ga miskinai……….”

  • Abuu Dawuuda (1609)
    -Ibnu Majah (1827)
  • al-Albaany, Sahiihul Jaami’ (3570)

Akwai wasu hadisan banda waɗannan biyun kan bayani ƙarara cewa abinci ake fitarwa ba kuɗi ba.

Ga wasu daga cikin “dalilai” ko shubuhohi na masu cewa ana iya bada kuɗi ba abinci ba, da kuma raddi a kansu.

Suna cewa:

1- Ai tunda maƙasudin bayar da zakkar ga talakawa shi ne a wadatar da su ga barin talauci da kuma roƙon mutane a wannan ranar, to ai kuwa kuɗi shi ne zai fi cancanta- wato ƙimar shi abincin.

Amsa:
To ai Annabi(SAW) ya san da wannan bukatar ta talakawan amma me ya sa bai ce a basu kuɗin ba? Ko babu talakawa ne a zamaninshi?
صلى الله عليه وآله وسلم؟
Wani hangen nesa ne masu wannan su ke da shi da babu irin haka a gun Mazon da Allah ke mishi wahayi?!!
2- Suna cewa idan kaba talaka abinci a matsayin zakkar fidda kai, to ina yaga kuɗin sarrafa shi abincin?

Amsa:
Sai nace to me zai hana ku haɗa mishi fa’idodi biyu: ku bashi zakkar abincin yanda Sunnah ƙarara kuma tabbatacciya ta umarta sannan kuma sai ku haɗa mishi da kuɗin a matsayin taimako da agaji, in dai da gaske ne taimaka mishi a ke so a yi?

3-
Ai cikin manya magabata – Allah Ya rahamshe su- akwai masu irin wannan fahimtar.

Amsa: Shin akwai wani magabaci da yake da gabata sama da gabatar Annabi Muhammad(SAW) Abinda Allah Yace shi ne:
“Duk abinda Manzo(SAW) yazo muku da shi ku riƙe, kuma duk abinda ya hane ku ga barinshi …al-Qur’ani 59:7
Na ke cewa, shin Allah Maɗaukaki a nan Ya ce: “duk abinda magabata suka zo da shi ku riƙe”?!!!
Akwai azanci wajen barin zancen wanda a ke mishi wahayi kuma “Ma’suumi”zuwa ga ijtihadin wanda yake ba ma’suumi ba?

Dan haka, ra’ayi kawai cewa wai a iya bayar da kuɗi madadin abinci.

Allah Ya saka ma wanda ya faɗi wannan baiti na waƙe a ƙasa domin kuwa baitin ya dace da wannan gaɓar. Yana cewa:

دعوا كل قولٍ عند قول محمدٍ
‏فما آمنٌ في دينه كمخاطرِ

Ma’ana:

“Ku ajiye zancen kowa idan yaci karo da zancen Annabi Muhammad
صلى الله عليه وسلم
Ai wanda yake da dahir kan addininshi ba kamar mai kasadar ɗauko abinda ba shi da tabbas ba ne”

Allah Ka ƙara mana ganewa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates