Ambaton Allah yana daga cikin aiki mai ɗinbin lada sannan kuma bashi da wahalar aikatawa ga wanda Allah ya datar dashi, domin mutum zai iya yinsa a kowani lokaci, kuma acikin kowani irin yanayi ba tare da ya gaji ba inhar ya zamto Zikirin yayi shi be a bisa tafarkin da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar.
Yau zamuyi magana akan wani zikiri ne mai girman falala da kuma girman lada.
Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito hadisi daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:
مَن قالَ: لا إلَهَ إلَّا اللَّهُ، وحْدَهُ لا شَرِيكَ له، له المُلْكُ وله الحَمْدُ، وهو علَى كُلِّ شيءٍ قَدِيرٌ، في يَومٍ مِئَةَ مَرَّةٍ، كانَتْ له عَدْلَ عَشْرِ رِقابٍ، وكُتِبَتْ له مِئَةُ حَسَنَةٍ، ومُحِيَتْ عنْه مِئَةُ سَيِّئَةٍ، وكانَتْ له حِرْزًا مِنَ الشَّيْطانِ يَومَهُ ذلكَ حتَّى يُمْسِيَ، ولَمْ يَأْتِ أحَدٌ بأَفْضَلَ ممَّا جاءَ به، إلَّا أحَدٌ عَمِلَ أكْثَرَ مِن ذلكَ
Bukhari: 3293
Wanda yace “La’ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai’in kadir” A cikin ranar shi sau ɗari, zata zamto masa kaman ladan ƴanta bayi ɗari, za’a kuma rubuta masa lada ɗari, za’a kuma kankare masa zunubi ɗari, kuma zata zamto masa kariya daga shaiɗan a wannan ranar tashi har sai ya wayi gari, kuma babu wanda zaizo da wani abu fiye da wanda yazo dashi sai dai wanda yayi fiye da tashi
Haƙiƙa Falalar Allah tana da yawa akan bayinsa, irin wannan garaɓasa ba abinda duk wani Mai hankali zai barta ta wuce bane. Ya kamata mu lazimci wannan zikirin a kullum, ba wahala take dashi ba, ta gama cin lokaci taci minti goma. Kada muyi wasa irin wa’innan falalolin su rinƙa wuce mu. Allah yasa mudace.
Leave a Reply