Ya ƴar’uwa ki sani cewa babu abinda ya fi miki ƙima irin kare mutuncinki da tsarƙaƙe kanki ga barin Aikata zina, domin ƙimar ki da mutuncinki yana tattare da kame kanki. Da zarar kin bada kanki, kin zubar da mutuncinki toh zaki zamto baki da ƙima a idon Al’ummah, da wanda ya san abinda kika aikata da wanda bai sani ba.
Ki sani cewa wanda yake ganinki da ƙima da mutunci bazai taɓa nemanki da alfasha ba.
Da zarar kinga mutum yana nemanki da aikata wannan mummunan laifi toh ki guje shi kuma ki nemi tsarin Allah daga gareshi domin ba mutumin kirki bane.
Duk lokacin da kika bada kanki ga ɗa na miji toh ƙimarki zata zuba a idonsa, koda ko ya aure ki bayan haka toh wannan taɓo ba zata taɓa gushe wa a zuciyarsa ba, sannan kuma zargi zaiyi ta shiga tsaƙaninku.
Ki sani da yawa daga cikin maza har in suka samu biyan buƙatar su daga ƴa mace toh ba kasa fai suke yarda su aure ta ba bayan haka. Sukan koma ne su nemi wacce suke gani tana kamun kai su aura, ke kuma a barki da nadama.
Ki saka acikin ranki a kullum cewa Babu wani mutumin kirki da zai nemi aikata alfasha dake! Toh in haka ne shin zaki yarda Fasiki ya zame miki abokin zama na har abada?
Leave a Reply