Darasi na Biyu a wannan shiri namu na Auratayya a wannan Tasha tamu mai albarka. Malam zaiyi mana nasiha akan Hikimar yin aure:
- Duk wanda yayi aure yabi Allah (S.W.T).
- Ka saka a ranka don Allah (S.W.T) da kuma koyi da Sunnar Annabi (S.A.W) za kayi aure.
- Aure yana kawar da sha’awa kuma yana runtse ido
- Aure yana tsare mutumdaga fadawa al fasha.
- Aure yana rage yaduwar alfasha, ‘ya’ya marasa uba yana kuma rage yaduwar cututtuka a cikin al’umma.
- Aure yana kara yawaitar al’umma na gari.
- Samun lada sanadiyyar mu’amalar aure da matarka.
- Duk wanda yayi aure to ya so kuma ya dabbaka abinda Annabi (S.A.W) ya ke so.
- Samun da ko ‘ya wanda za suke maka addu’a ko bayan ka mutu.
- Wanda ya haifi yaro ya mutu yana karami to yaron zai ceci iyayensa ranar Alkiyama.
- Samun ziriyyar da za ta tallafawa addinin Musulunci.
- Samun nutsuwa, kwanciyar hankali da kuma makoma ingantacciya.
Download
Leave a Reply