003 Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar 11 January 2020

Danna nan domin shiga karatu Online

Shimfida Ka karɓi gaskiya ko da wanda ya zo maka da ita maqiyanka ne na nesa, ka mayar da qarya ko da wanda ya zo maka da ita masoyinka ne na kusa. Ka da kazauna da mutane sai akan gaskiya, kada ka yi sha’awar abinda ka gani tare da mai rai sai abinda da za ka yi sha’awa tare da matacce_” Ubay bin Ka’ab (Allah ya yarda da shi)


Tambayoyin dake ciki:

  1. Hukuncin aikin karbar haraji ma gwamntin da ta ke da kudin da za zata iya yi ma qasarta aiki.
  2. Hukuncin shari’a yayin da mace ta yadda ta yi zina amma wanda yayi mata bai yadda ba!
  3. Shin saki ya auku ga wanda ya kudurce ya saki matanshi amma bai furta mata, kuma bai bata takarda ba?
  4. Mutane biyu da su ka rasa sallar jum’a ya hallata su yi jam’i?
  5. Hukuncin sanya jajaye ko rawayar kaya ga mata da maza?
  6. Shin hadisin Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) da ya ruwaito cewa duk wanda ya fadi La’Ilaha Illahu Wa Subhannallahi WabiHamdihi sau dari yana da lada mai girma ya inganta?
  7. Safan da ya kamata a yi shafa akai?
  8. Hukuncin wanda ya sinci kudi bai yi cigiya ba.
  9. Yadda ake yin nafila raka’a hudu. za a karanta fatiha da sura a raka’oi biyu na qarshe?
  10. Ɗa ya na iya rama ma mahaifinshi sallah da bai yi ba saboda rashin lafiya?
  11. Yaya ma’aikacin da yake aiki a Kaduna-yayi aure a Kaduna zai yi rabon kwana da matanshi da take zama a Katsina?
  12. Shin ba a nafila daga bayan sallar jum’a zuwa sallar la’asar?
  13. Ana iya rama raka’a biyu da ake yi kafin sallar la’asar?
  14. Matsayin auren da mutum bai gaya ma wasu daga cikin danginsa ba!
  15. Ya hallata tahiyyatul masjid a harabar massalacin jum’a yayin da liman ya ke huduba?
  16. Shin siffar wankan Juma’a iri daya ne da wankan janaba?
  17. Ya tabbata a hadisi cewa Annabin Rahma ya ga Allah?
  18. Ana yin sallama ma masu karatu ko cin abinci?
  19. Menene falalar yin azumin 13,14, 15 na kowacce wata? Kuma azumtar kwanaki ukun yafi yin azumin litinin da al-khamis?
  20. Yaya macen da take nakuda, tare da fitar da farin ruwa tsawon kwana uku zata yi, ko rama sallolin wadanan ranaku?
  21. Wanda yayi bakance zai iya sauke bakancen da yayi?
  22. Yaya makaracin al-qur’ani zai yi salati in ya biyo kan ayar da aka ambaci sunan Annabi Muhammad (saw)?
  23. Banbancin baiwa da sadaka?
  24. Ya halatta marar lafiya yaqi shan magani don Allah ya kankare mishi zunubansa?
  25. Ya tabbata hada salloli lokacin sanyi?

Download

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “003 Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar 11 January 2020”
  1. […] 11 January 2020 05 January 2020 04 January 2020 […]

Leave a Reply

Categories
Latest updates