Fatawowin Rahama by Dr. Sani Umar 07-December-2019

Fatawa

Shimfida- “ Qasa zata amayo guntattakin abin cikinta na zinari da azurfa, manya manya kaman ginshikai – sai wanda yayi kisa yace a saboda wannan ne na yi kisa; sai wanda ya yanke zumunci shima ya ce a saboda wannan ne ya yanke zumunci; sai wanda yayi sata ya zo yace akan wannan ne aka yanke hannun shi. Sannan su bar wannan dukiyan duka ba mai ta6a komai a cikinta”.


Tambayoyi dake ciki:

 1. Ya hallata mutum ya ci danyen kifi?
 2. Nasiha ga wadda take son ta yi sallah amma bata iya yin sallar.
 3. Wai da gaske ne ba Nana ‘A’isha (RA) akai yi wa qazafin zina ba?
 4. Wanda ya taba laifi ya tuba, zai iya rantsuwa ma wanda su ke cigaba da żargin shi akan wannan laifin?
 5. Hukuncin wanda yayi bakance in Allah ya biya mishi wata buqatar shi zai gabatar da wani aikin alkhairi, bai aikata aikin alkhairin ba saboda buqatar bata samu ba!
 6. Sahihancin samu ko rashi – jarabawa ce daga Allah.
 7. Hukuncin wadda ta sha azumi saboda ciki da shayarwa, ta kasa ramawa saboda rashin lafiyar ulcer- za ta ciyar a kowanni lokaci ko sai watan axumin ya tsaya, ko ciyarwar ta fadi?
 8. Shin bismilla ko sallama mutum zai yi idan zai aika saqon wasiqa ko text?
 9. Yadda za a fitar da zakkar kudin da mutum ya samu ta sana’ar hannu da kudin da ya samu na balance din a daidaita sahu!
 10. Hukuncin kudin da aka ba ma ma’aikacin gwamnati saboda amfani da qwarewarsa a samu wata takarda ko amfani -kamar driver’s licence.
 11. Ya hallata amfani da mushafin al-qur’ani a shirin film?
 12. Hallacin sayayya a ranar black friday?
 13. Mutumin da ya je hajji bai yi aski ba yana da laifi?
 14. Gwargwadon abinda mace zata cire a gashinta ya zama tayi aski karbabbe ma hajjinta.
 15. Ya hallata mamu ya dauki al-qur’ani lokacin sallar tahajjud ko tarawih?
 16. Matsayin masu fadin “ Bala wa nahnu ala dhalika mina shahidin” a qarshen suratut Tin.
 17. Hukuncin wanda ya gina gidan kallon bal domin sana’a.
 18. Hukuncin “hire purchase”
 19. Hukuncin yin salati a sallar farilla?
 20. Shin miji zai iya zuwa ma kowacce matanshi ya ga dama duk lokacin da ya so, ba tare da la’akari da rabon kwana ba saboda fadin Allah (SWT) “ matayenku gonaki ne a gare ku, don haka ku je wa gonakinku ta inda kuka so…”

Download

Click Here to Support our work

One Comment

Leave a Reply

%d bloggers like this: