SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI”
Daga Muhammad Rabiu Umar
Dalilin Yin Wakar “Ni Dai Barhama Nake Bautawa, Don Shi Ya Halicce Ni”
A yan kwanakin nan wata waka da wani mawaki ya yi mai take “Ni dai Barhama nake bautawa, don shi ya halicce ni” ta jawo cece-kuce a tsakanin mutane, kuma da yawa daga cikin mutane sun yi mamakin a ce wai musulmi ne ya yi wannan wakar, wanda daga baya-bayan nan gwamnatin Kano ta hanyar hukumar tace finafinan ta bada sammacin a kamo wannan mawaki.
Amma alal-hakika duk wanda ya san irin akidar da take cikin manya-manyan littattafan darikun sufaye – musamman yan tijjaniyya – to ba zai yi mamakin jin irin wannan waka ta fito daga irin masu wannan darika.
Idan muka dauki babban littafin darikar tijjaniyya mai suna “Jawahirul Ma’ani” zamu ga cike yake da akidar “Komai Allah ne” ma’ana duk wani abu da yake duniyar nan Allah ne, kuma in an bauta masa babu laifi, Allah aka bautawa, ga kadan daga cikin abin da ya zo akan haka : Shehu Tijjani ya ce :
“فما في ذوات الوجود كله إلا الله سبحانه وتعالى تجلى بصورها وأسمائها، وما ثمّ إلا أسماؤه وصفاته” (جواهر المعاني : 1/259).
Ma’ana “Babu abin da yake cikin zatin dukkan samammu gaba dayansu sai Allah Subhanahu Wa Ta’ala, shi ne ya bayyana a surarsu da sunayensu. Babu wani abu sai sunayensa da siffofinsa” (Jawahirul Ma’ani 1/259).
Wannan magana tana nuna cewa duk wani abin da yake samamme a wannan duniya to ba komai ba ne face Allah ne, saboda Allah ne ya bayyana a cikin dukkan komai da sunayensa da siffofinsa.
A wani wurin ya ce :
“إن جميع المخلوقات مراتب للحق…فإن الوجود عين واحدة لا تجزؤ فيها على كثرة أجناسها وأنواعها ووحدتها” (جواهر المعاني : 2/92).
Ma’ana : “Dukkan ababen halitta wasu yanki ne na Allah….saboda da dukkan samamme abu daya ne, babu wani yanki-yanki a cikinsa, duk da jinsinsa mai yawa da nau’o’insa da hadewarsa” (Aljawahir 2/92).
Wannan bayani yana nuna cewa duk wata halitta Allah ce ita, kuma komai da muke gani abu daya ne, wanda shi ne Allah!.
Ya sake cewa :
“فكل عابد أو ساجد لغير الله في الظاهر فما عبد ولا سجد إلا لله تعالى، لأنه هو المتجلي في تلك الألباس، وتلك المعبودات كلها تسجد لله تعالى…وقوله “لا إله إلا أنا” يعني لا معبود غيري وإن عبد الأوثان من عبدها فما عبد غيري” (جواهر المعاني : 1/184)
“Duk wani mai bauta ko mai sujjada ga wanin Allah a zahiri, ba wanda ya bautawa ko ya yi wa sujjada sai Allah Ta’ala, saboda shi ne yake bayyana a cikin wadannan abubuwa, kuma duk wadannan abubuwa da ake bautawa suna sujjada ne ga Allah (S.W.T)….sannan fadin Allah “Babu abin bautawa sai ni” yana nufin babu wani abin bautawa, wanda ba ni ba, ko da kuwa masu bautar gumaka sun bauta masu, ba su bautawa wani ba” (Jawahirul Ma’ani 1/184).
Wannan kadan kenan daga cikin mummunar akidar dake cikin wannan babban littafin na darikar tijjaniyya. To yanzu dan uwa mai karatu wanda ya karanta wadannan maganganu, kuma ya yi imani da su, ya yarda da cewa wanda ya yi su, waliyyi ne daga cikin waliyyan Allah, kuma duk abin da yake fada Annabi ne (S.A.W) yake fada masa, a farke a cikin barci, to yaya ba zai ce “Barhama Yake Bautawa ba”!.
Wata kila mai karatu ya ce, to ba Barhama ba ne ya koyar da haka, don haka me ya sa shi mai wakar bai ce “Shi Tijjani yake bautawa ba” sai ya ce Barhama.
Dalili, shi kansa Barhama din wato shehu Ibrahim Inyass haka shi ma ya koyar ya kuma kira muridansa da mabiyansa a kan haka, a cikin littattafansa, ga kadan daga cikin abin da ya fada a kan haka :
Yana cewa :
فإنّ الشّيخَ مظـهرُ ذات ربِّي وعينُ العَين عينُ أبي العباس. (( ديوان تحفة أطايب الأنفاس )) (ص86).
Ma’ana : Lallai hakika shehu shi ne Mazharin zatin Ubangijina. Kuma Hakikanin zati, shi ne zatin Abul Abbasi (wato shehu Tijjani).
Anan zamu ga Inyass yana cewa shehu Tijjani shi ne Allah, kuma duk wani zati na wani abu, ba komai ba ne face zatin shehu Tijjani, don haka komai shehu Tijjani ne, shi kuma Allah ne!!.
A wani wuri cewa ya yi :
خليفةُ الله في أرضٍ لذلك مَن رآكمُ قد رَأى ربَّ البريَّات
Ma’ana : “Khalifan Allah a bayan kasa, don haka duk wanda ya ganku, to lallai ya ga ubangijin halitta”. (Duba littafinsa Diwanu Tuhafatil Adayibil Anfas).
Subhanallahi, don ka ji mai karatu duk wanda ya ga shehu Tijjani to ya ga Allah, Ma’ana da Allah da Shehu Tijjani duk abu daya ne!!!.
Wannan kadan kenan daga cikin akidun da suke cikin littattafan wadannan sufaye, kuma a kansu ne suke kokarin renon mabiyansu, wanda har akwai wata tarbiyya da ake wa muridi, wadda bayan ya yi ta, sai zama Allah, kuma komai ya zama Allah a wurinsa, Sheikh Dahiru Mai gari (Allah Ya Yi masa Rahama) ya yi rubuta akan wannan tarbiyya da darika, ya tabbatar da wadannan abubuwa.
Don yan uwa in ana so a magance ci gaba da faruwar irin wadannan wakoki to dole ne sai an wancakalar da wadancan littattafai, kuma an dawo kan koyarwar Alkur’ani da Hadisi a bisa fahimtar magabata na Kwarai. Allah ya tsare mana Imaninmu Ameen.
Leave a Reply