Haƙiƙa ko wani Musulmi yana da sanin cewa Allah ka iya jarrabar sa a kowani lokaci, sannan ita jarabawa tana zuwa ne ko dun laifi da mutane sukayi, sai Allah ya sauƙar musu da bala’i domin suyi nazari su tuba, ko kuma dai Allah ya sauƙar da wannan bala’i domin gwajin Imanin masu imani.
Sai dai halin da mutane suke shiga yayin irin wannan jarabawar tana banbanta,wasu sukan miƙa ragamar komi zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, sannan suyi ƙanƙan da kai su roƙi Allah neman mafita, wasu kuma sukan dogara ne da ƙoƙarinsu da kuma iyawarsu su mance da Allah baki ɗaya, wasu kuma sukan rikice ne su mance da Allah su shiga damuwa da ɗimuwa a halin kuma babu abinda zasu iya yi.
Toh a irin wannan hali me ya dace Musulmi yayi? Sannan da wa ya kamata yayi koyi cikin wannan rabe raben mutane?
Dogaro ga Allah da maida ragamar komi gareshi: matakin farko da Musulmi ya dace ya ɗauka shine ya sami natsuwa sannan ya sani cewa wannan musiba da ta sauƙo daga Allah ne, sannan babu wanda ya isa ya yaye ta sai Allah maɗaukakin sarki, duk wani abinda za’ayi in Allah bai ga daman yaɗa ta ba babu wanda ya isa ya yaɗa ta. Sannan duk wani matakan kariya da mutum zai ɗauka in Allah ya nufi cewa wannan Annoba zata sameshi toh babu makawa sai ta sameshi. Sabida haka a irin wannan lokaci kada mutum ya yarda ya mance da Allah, yana da kyau mutum ya ɗauki matakan kariya wanda masana suka yi kira da abi su. amma kada ya zamto ya dogara kacokam kan wannan sababin.
Allah yace:
ما أصاب من مصيبة إلا بإذن الله ومن يؤمن بالله يهد قلبه والله بكل شيء عليم
Babu wata musiba da zata sami wani sai da izinin Allah, wanda yayi Imani da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa, Allah masanin komai ne.
Addu’a da istigfari sune ƙashin bayan kawar da annoba: mataki na biyu shine lazimtar addu’a, da ƙanƙan da kai zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, sannan kuma mu lazimci istigfari.
Allah maɗaukakin sarki yace:
ولقد أرسلنا إلى أمم من قبلك فأخذناهم بالبأساء والضراء لعلهم يتضرعون.
فلولا إذ جاءهم بأسنا تضرعوا ولكن قست قلوبهم وزين لهم الشيطان ما كانوا يعملون
الأنعام ٤٢-٤٣
Haƙiƙa mun aika da manzanni zuwa ga Al’ummomi da suka gaba ce ka, sai suka kafirce sai muka kama su da talauci, da cututtuka domin ko zasuyi ƙanƙan da kai su koma zuwa ga Allah. Ina ma ace lokacin da azabar mu tazo musu sunyi ƙanƙan da kai sun koma zuwa ga Allah! Amma sai suƙa ƙi, suka bijire, zuƙatansu suka ƙeƙashe, shaiɗan ya ƙawata musu munanan ayyukan su.
Al-An’am 42-43
Wannan aya tana nuna mana cewa abinda ya dace muyi shine muyi ƙanƙan da kai mu koma zuwa ga Allah, domin da haka ne Allah zai yaye mana wannan musiba, amma idan muka ƙi yin haka toh haƙiƙa zamu taɓe, sannan Allah zai barmu cikin ruɗanin mu. Sannan mu yawaita yin istigfari, domin yawaita istigfari yana daga cikin sabbuban yaye musiba.
Mu guje wa yaɗa jita jita: a irin wannan lokaci jita jita na yawaita, ya kamata Musulmi ya sani cewa yaɗa jita jita haramun ne a Musulunci,kada ka yadda ka yaɗa wani abu sai ka tabbatar da ingancin sa, domin zaka iya yaɗa wani abu da zai zamto sanadiyyar cutar da wani ko Salwantar da ransa, kamar yadda ya faru a lokacin Cutar Ebola, mutane suka rinƙa shan gishiri wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu. Toh a lokacin da ka yaɗa labarin ƙarya wani yayi amfani dashi ya cutu ka sani laifi na wuyanka.
Mu lazimci Azkar da suka zo daga Manzon Allah na neman kariya: Akwai zikirori ingantattu da suka zo daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama domin neman kariya, ya wajaba akan musulmi ya koyesu, sannan ya kiyaye su a kowani lokaci. Ga wasu daga cikinsu:
مَنْ قَالَ : بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ لَمْ تُصِبْهُ فَجْأَةُ بَلَاءٍ حَتَّى يُصْبِحَ ، وَمَنْ قَالَهَا حِينَ يُصْبِحُ ثَلَاثُ مَرَّاتٍ لَمْ تُصِبْهُ فَجْأَةُ بَلَاءٍ حَتَّى يُمْسِيَ
Bismillahi llazi la yadurru ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama’i wa huwa ssami’ul Aleem Sau uku safe da yamma.
عَن خَوْلَةَ بِنْت الحَكِيمِ قالت: سمعت رَسُولِ الله -صلى الله عليه وسلم -يقَولَ: «مَنْ نَزَلَ مَنْزِلاً فقَالَ أَعُوذُ بِكلِمَاتِ الله التّامّاتِ مِن شَرّ مَا خَلَقَ لَمْ يَضُرّهُ شيءٌ حَتّى يَرْحَلَ مِنْ مَنْزِلِهِ ذَلِكَ
A’uzu bi kalimatillahi ttamat min sharri ma khalaka. Mutum zai karanta duk inda yaje.
اللهم إني أعوذ بك من البرص والجنون والجذام ومن سيئ الأسقام
Allahumma inni A’uzu bika minal barasi, wal jununi, wal juzami, wamin sayyi’il asƙami
Bayan wa’innan addu’oi mutum ya dace ya lazimci duk wani addu’a da ta inganta daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama domin neman kariya, kaman Zikirin safe da yamma. Domin da haka ne mutum zai sami kariya. Domin babu wani abu da zai sami mutum sai da izinin Allah, idan mutum ya roƙi Allah yayi ƙanƙan da kansa sai Allah ya amsa masa ya kuma kareshi.
Sai kuma zuwa ga likitoci Musulmi. Wannan lokaci ne da Al’umma suke da matuƙar buƙatar ku, ya dace ku jajirce ku kyautata niyya wurin taimakawa Al’umma ta yadda duk zaku iya. Kuyi hakan da kyakkyawan niyya Allah zai baku lada mai girma. Allah yasa mudace, ya kare mu baki ɗaya daga wannan cuta, ya kuma kawo mana ƙarshen sa.
Leave a Reply