An rawaito daga Abu Sa’eed Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan yayi sabon tufa ya kan kirashi da sunansi sannan yace:
اللَّهمَّ لك الحمدُ أنت كسوْتنِيهِ أسألُك من خيرِه وخيرِ ما صُنِعَ له ، وأعوذُ بك من شرِّهِ وشرِّ ما صُنِعَ له
Allahumma lakal hamdu Anta kasautanihi, As’aluka min khairihi wa khairi ma suni’a lahu, wa A’uzu bika min sharrihi wa sharri ma suni’a lahu
Abu dawud: 4020
Turmidhi: 1727
Sharhin Addu’ar:
Ubangijina ina maka godiya kaine ka azurtani da wannan tufafi, ba tare da iyawa ta ba, ina roƙon ka ka sanya wannan tufafi ya zamto mai taimako na wurin aikata alheri, Ka haɗa ni da alherinsa, ina kuma neman tsarinka daga sharrinsa sa: ka kiyaye ni kada ya zamto wannan tufafi ya zamto sanadiyyar saɓa maka.
Leave a Reply