Wata rana Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya shigo masallaci sai ya iske wani daga cikin Ansar ana kiransa Abu Umama yana zaune, sai Annabi yace ya naganka a zaune a masallaci kuma ba lokacin sallah ba?
sai yace: damuwa ce da bashi sukayi min yawa ya Manzon Allah.
sai Annabi yace: bazan koya maka wani addu’a wanda idan kayi shi Allah zai yaye maka damuwarka ya kuma biya maka bashinka ba?
Abu umamah yace: Sanar dani ya Manzon Allah.
Sai Annabi yace: kace duk lokacin da ka wayi gari, da lokacin da kayi yammaci,
Allahumma inni A’uzu bika minal hammi wal huzn, wa a’uzu bika minal ajzi wal kasal, wa A’uzu bika minal jubni wal bukhl, wa A’uzu bika min galabatid-daini wa Qahri rijal.
Sai Abu umamah yace: na karanta wannan Addu’ar sai Allah ya yayemin damuwa dake damuna, ya kuma Bani daman fita daga bashin da ake bina.
Fassarar Addu’ar:
Allah ina roƙon ka tsari daga damuwa, da kuma baƙin ciki, ina kuma neman tsarin ka daga gazawa da kasala, ina kuma neman tsarin ka daga Ragwanta da kuma rowa, ina kuma neman tsarin ka daga Yawan bashi da kuma galabar maza(Ma’ana su samu galaba a kaina).
Abu dawud: 1555.
Nassin Hadisin:
دخل رسولُ اللهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم ذاتَ يومٍ المسجدَ فإذا هو برجلٍ من الأنصارِ يُقالُ له أبو أمامةَ جالسًا فيه فقال يا أبا أمامةَ ما لي أراك جالسًا في المسجدِ في غيرِ وقتِ الصَّلاةِ قال همومٌ لزِمتني وديونٌ يا رسولَ اللهِ قال أفلا أُعلِّمُك كلامًا إذا قُلتَه أذهب اللهُ عزَّ وجلَّ همَّك وقضَى عنك ديْنَك فقال بلى يا رسولَ اللهِ قال قُلْ إذا أصبحتَ وإذا أمسيْتَ اللَّهمَّ إنِّي أعوذُ بك من الهمِّ والحزنِ وأعوذُ بك من العجزِ والكسلِ وأعوذُ بك من البخلِ والجبنِ وأعوذُ بك من غلبةِ الدَّينِ وقهرِ الرِّجالِ قال فقلتُ ذلك فأذهب اللهُ عزَّ وجلَّ همِّي وقضَى عنِّي دَيْني
Leave a Reply