AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB NE SHI KO KUWA WANINSA: (I)(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

1. Ya kamata a san cewa aqidar Ahlus Sunnah wal Jama’ah ita ce: Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib -Allah Ya kara masa yarda- Sahabi ne babba mai yawan daraja. A kuma san cewa abin da ake nufi da Sahabi shi ne: wanda ya samu haduwa da Annabi mai tsira da amincin Allah alhalin yana mumini kuma ya mutu yana mai imani. A kuma san cewa abin da ake nufi da munafuki shi ne: mutumin da ya bayyanar da Musulunci da nuna biyayya ga manzon Allah mai tsira da amincin Allah amma kuma yake boye kafurci cikin zuciyarsa. A kuma san cewa yana daga cikin aqidar Ahlus Sunnah wal Jama’ah nuna kauna da soyayya ga dukkan sahabban manzon Allah mai tsira da amincin Allah; saboda su ne suka fi kowa cikar imani da ihsani, suka fi kowa yawan da’ah da jihadi, Allah kuma Ya zabe su da abokantakar annabinSa mai tsira da amincin Allah, babu kuma wani da zai zo daga bayansu da darajarsa za ta kai tasu. A kuma san cewa su Sahabbai dukkansu adilai ne; saboda irin yadda Allah da manzonSa suka bayyanar da adalcinsu, kuma su waliyyan Allah ne zababbu cikin halittarSa, kuma su ne suka fi kowa daraja cikin wannan Al’ummah, babu wani da ya fi su daraja in banda manzon Allah mai tsira da amincin Allah; daga cikin abin da ke tabbatar da wannan magana tamu shi ne fadar Allah Madaukaki cikin suratut Tauba aya ta 100 inda Ya ce: 
((Na farko wadanda suka tsere wa kowa daga cikin Muhajirai, da Ansarawa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautayi, Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi, kuma Ya yi musu tattalin gidajen Aljannah da korumma ke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har a bada, wannan kuwa shi ne rabo mai girma))

Lalle yi wa Sahabbai shaidar kwarai abu ne tabbatacce cikin addinin Musulunci, sannan nuna musu soyayya da kauna bangare ne na addini da imani, kamar yadda nuna musu kiyayya yake bangare ne na kafurci da munafurci; wannan shi ne ya sa su Ahlus Sunnah wal Jama’ah ba sa ambaton su sai tare da girmamawa da jinjina. Sannan yana da kyau a san cewa dukkan Sahabbai kusan dubu daya da dari hudu (1,400) da suka halarci mubaya’ah a karkashin Itaciya a waqi’ar Hudaibiyyah a watan Zul Qa’adah a shekarar hijira ta shida, dukkansu Allah Ya yarda da su, babu daya daga cikinsu da zai shiga Wuta gobe Kiyama; saboda Allah Ya ce cikin suratul Fathi aya ta 18: 
((Hakika Allah Ya yarda da Muminai a lokacin da suke maka mubaya’a a karkashin Itaciya, kuma Ya san abin da ke cikin zukatansu, Ya saukar da nitsuwa a kansu, Ya kuma yi musu sakayyar wani budi makusanci)). Haka nan Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 4,655, da Imamut Tirmiziy hadithi na 3,860, da Imamu Ahmad hadithi na 14,820, da Ibnu Hibban hadithi na 4,802 da isnadi sahihi daga Jabir Bin Abdullah, daga manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Babu mutum daya cikin wadanda suka yi mubaya’a a karkashin Itaciya da zai shiga Wuta)). A kuma san cewa su Ahlus Sunnah wal Jama’ah ba sa zagin kowa daga cikin Sahabbai saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya haramta musu hakan; Imamul Bukhariy ya ruwaito hadithi na 3,470, da Imamu Muslim hadithi na 2,540 daga Abu Sa’id Al-Khudriy, da Abu Hurairah Allah Ya kara musu yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Kada ku zagi sahabbaina, kada ku zagi sahabbaina, ina rantsuwa da wanda raina ke hannunSa da dayanku zai ba da sadakan zinarin da nauyinsa ya kai nauyin dutsen Uhdu, to da wannan ba zai kai mudun dayansu ko rabin mudun dayansu ba)). A kuma san cewa su Ahlus Sunnah wa Jama’ah suna ganin cewa: Abubakar, da Umar, da Uthman, da Aliyyu su wadannan Sahabbai hudu su ne Khulafaa’ur Rashidun a bisa wannan jeri nasu, kuma su ne suka fi ko wane Sahabi daraja, kuma su ne na gaba cikin Sahabbai goman nan da aka yi musu bushara da Aljannah tun daga nan Duniya, kuma a cikinsu ne tare da sayyidina Hasan jikan Annabi Khilafar Annabci ta shekara talatin take; saboda hadithi na 2,226 da Tirmiziy ya ruwaito, da na 8,155 da Nasa’iy ya ruwaito, da na 21,978 da Ahmad ya ruwaito da isnadi sahihi daga Safeenah Allah Ya kara mata yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Khilafah a cikin al’ummata shekaru talatin ne, daga nan sai mulki bayan hakan)). A kuma san cewa su Ahlus Sunnah wa Jama’ah suna kaunar Ahlul Baiti watau iyalan Annabi mai tsira da amincin Allah: danginsa na jini da kuma matansa; saboda hadithi na 6,378 da Imamu Muslim ya ruwaito daga Zaid Bin Arqam Allah Ya kara masa yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Ina tunatar da ku Allah game da iyalan gidana, ina tunatar da ku Allah game da iyalan gidana)). Da kuma hadithi na 6,077 da Imamu Muslim ya ruwaito daga Waathilah Bin Al-Asqa’a Allah Ya kara masa yarda ya ce: ya ji manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana cewa: ((Lalle Allah Ya zabi Kinaanah daga cikin ‘ya’yan Isma’il, Ya kuma zabi Quraish daga cikin Kinaanah, Sanan Ya zabi Banu Hashim daga cikin Quraish, Ya kuma zabe ni daga cikin Banu Hashim)). Sannan Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin suratul Ahzab aya ta 32-33 ((Ya ku matan Annabi ba daya kuke da sauran mata ba, idan kuka yi takawa, kada ku sassutar da magana har wanda cuta ke cikin zuciyarsa ya yi wani tsammani, ku fadi magana mai karimci. Ku zauna cikin gidajenku kada ku yi fita irin ta jahiliyyar farko, ku tsaida salla, ku bayar da zakka, ku yi da’a wa Allah da manzonSa, Allah dai na nufin tafiyar da kazanta ne ga barinku Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa, ya ku ahlul Baiti)). A nan Allah da kanSa ne Ya kira matan Annabi da cewa su ahlul Baiti ne, ke nan duk wanda ya ci mutuncinsu lalle ya ci mutuncin Annabi, ya kuma ci mutuncin ahlu baitinsa. Wannan aqidah ita ce tabbatacciyar aqidar Ahlus Sunnah wal Jama’ah.
2. Lalle misalin ahlus Sunnah wal Jama’ah, da misalin Shi’ah Rafidah a bangaren kare gaskiya da bangaren kare karya, kamar misalin Musulmi ne da Kiristoci, Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin littafinsa mai suna Minhaajus Sunnatin Nabawiyyah fi Naqdhi Kalaamish Shii’atil Qadriyyah 2/55-57 ya ce: ((Ahlus Sunnah tare da Raafidha kamar Musulmi ne tare da Kiristoci; lalle su Musulmi suna yin imani da cewa (Isa) Almasihu bawan Allah ne kuma manzonSa ne, ba sa wuce gona da iri game da shi irin wuce gona da iri na Kiristoci, ba sa kuma yin masa jafa’i irin jafa’in Yahudawa. Kiristoci suna ikirarin allantaka gare shi kuma suna son su fifita shi a kan (Annabi) Muhammad, da (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Musa, kai suna ma fifita Hawaariyaawa (almajiran Isa Almasihu) a kan wadannan Manzanni, kamar yadda (Shi’ah) Rafidawa ke son fifita wadanda suka yi yaki a gefen Aliyyu; irin Muhammad Bin Abibakr, da Ash’tar An-Nakha’iy a kan (Khalifa) Abubakar, da (Khalifa) Umar, da (Khalifa) Uthman, da ma mafi yawan Sahabbai daga cikin Muhajirai, da Ansarawa. Musulmi idan yana mukabala da kirista ba yi da ikon ya fadi wani abu game da (Annabi) Isa sai abin da yake shi ne gaskiya, to amma idan kana son ka san jahilcin kirista, ka san cewa ba yi da wata hujja tare da shi, to ka kaddara gudanar mukabala tsakaninsa da bayahude; lalle ba zai yiwu ba ga kirista ya ba da amsar shubuhohin da bayahude zai fiskantar masa, sai da irin amsar da Musulmi zai bayar (domin ture shubuhohin da shi kirista zai fiskantar da su zuwa gare shi). In har (shi kirista) ya ki shiga addinin Musulunci to kuwa dole ne ya kasa ba da amsar shubuhohin bayahude; saboda idan aka umurci kirista da yin imani da (Annabi) Muhammadu mai tsira da amincin Allah sannan ya soki annabcinsa da wani abu daga cikin abubuwa, to ba zai yiwu ya fadi wani abu na suka a kan (shi Annabi Muhammad) ba, face bayahude ya fadi wani sukan da yafi nasa girma a kan (Isa) Almasihu; saboda hujjojin da suke nuna (manzancin) Muhammadu karfinsu ya dara hujjojin da suke nuna (manzancin Isa) Almasihu, kuma nisantar al’amarin (Annabi) Muhammad daga shubuha ya fi nisantar (Isa) Almasihu daga shubuha; saboda haka idan har suuka za ta halatta a kan abin da hujjarsa ta fi girma kuma al’amarinsa ya fi zama nesa da shubuha, to kuwa halaccin yin suuka a kan abin da bai kai shi ba shi ne ya fi cancanta. Idan kuma yin suuka a kan (Isa) Almasihu kariya ce marar hujja, to lalle yin suka a kan (Annabi) Muhammad shi ne ya fi zama kariya mara hujjar kamawa; domin idan har shubuhar da ta fi karfi za ta karye, to raunannar shubuha ita ce ta fi cancantar karyewa, idan kuma hujjar da wata hujjar ta fi ta karfi ta tabbata, to lalle hujjar da ta fi karfin ita ce ta fi cancantar tabbata; saboda haka ne ma da yawa daga cikin mukabalar da Musulmi ke yi da Kiristoci suna yin ta ne a bisa wannan tsari; kamar sananniyar hikayan nan ne daga Khadhi Abubakr Bin Tayyib (Al-Baaqillaaniy a lokacin da Musulmi suka tura shi (watau sarkin Musulmi Adhudin Daulah Fanna-Khus’ruu Bin Buwaih Ad-Dailamiy) ya tura shi zuwa ga sarkin Kiristoci (na Rumawa) a Qustantiniyyah (a lokacin da ya isa can) sun girmama shi, lalle su Kiristocin sun nuna suna sane da darajarsa; wannan ya sa suka ji tsoron (kada ya karya musu tsarin da ake bi a gaban sarkinsi watau) ya ki yi wa sarki sujjada in ya shigo (fada) saboda haka ne ma sai suka shigo da shi ta wata karamar kofa ta yadda in zai shigo to zai shigo ne yana mai durkusawa, to amma sai ya fahimci dabararsu, da ya zo shiga sai ya shigo ta baya-baya yana mai ba wa (Sarki) kugunsa, watau sai ya yi (musu) sabanin abin da suke son ya yi a (gaban sarkinsu). To a lokacin da ya zauna (a gaban Sarki) sai suka yi masa magana, kuma wani sashinsu ya so yin suka ga (al’ummar) Musulmi, ya ce da shi: Mene ne kam ne aka ce game da A’isha matar annabinku? watau yana son ya bayyanar da kiren kariyan nan (a kan Nana A’isha) da (Shi’ah) Rafida ke yi. Sai Khadi (Al-Baaqillaaniy) ya ce: Wasu mata biyu ne aka soka, aka jefe su da zina a bisa tsabar kariya: Maryam da A’isha; amma ita Maryam ta zo da yaro tana rike da shi ba kuma tare da miji ba, ita kuwa A’isha ba ta zo da yaro ba, sannan kuma tana da mijinta, (da wannan) sai aka rufe bakin Kiristoci. Ma’anar maganar (Khadi Al-Baaqillaaniy) ita ce: bayyanar kubutar (Nana) A’isha (daga yin zina) ya fi bayyanar kubutar (Nana) Maryam (daga yin zina), kuma shubuhar yin zina ta fi kusa da (Nana) Maryam a kan (Nana) A’isha; idan kuma duk da haka kariyar masu sukan (Nana) Maryam (da yin zina) ta tabbata (a fili), ke nan kariyar masu sukan (Nana) A’isha (da yin zina) ita ta fi dacewa da tabbata)). Intaha.
3. Wannan shi ne kashin farko na rubutunmu, in sha Allahu Ta’ala kashi na biyu na nan tafe. Allah Ya taimake mu Ya tsare mu daga sharrin dukkan masu sharri. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates