ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN
DA ALLAH YA HALITTA,
BA WAI HASKEN MANZON
ALLAH KO ZATINSA BA, KAMAR
YADDA MASU BIDI’A KE CEWA
BA:
Sau da dama ‘Yan’uwa Musulmi za
ku rika ganin cewa Sufaye da
dukkan wadanda suka saki hanyar
Shari’ah cikin tafiyar da addininsu
suna barin yin aiki da nassin
Alkur’ani, ko nassin ingantaccen
hadithi, su koma suna yin aiki da
nassoshin da ko dai su ne suka
kirkiro su da kansu, ko kuwa a’a
wasu hadithai ne masu rauni
matuka, ko kuwa wasu hadithai ne
na karya a bisa ittifakin masana
ilmin hadithi!!
Misali: Imam Abu Daawuud ya
ruwaito hadithi na 4,702, da
Imamut Tirmizi hadithi na 2,155, da
Imam Ahmad hadithi na 22,757
daga Sahabi Ubaadatu Dan
Saamit, haka nan ma Imamul
Haakim cikin Mustadrak dinsa
hadithi na 3,693, da Imamut
Tabaraanii cikin Almu’ujamul
Kabeer hadithi na 12,060, da
Imamul Baihaqii cikin As-Sunanul
Kubraa hadithi na 18,157 daga
Sahaabi Abdullahi Dan Abbas,
sannan Imamul Albaanii da sauran
masana Ilmin Hadithi sun inganta
shi, dukkan wadannan Sahabbai
biyu ko wannensu ya ce:-
(( ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ:
ﺍﻥ ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﻠﻢ، ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ: ﺍﻛﺘﺐ. ﻗﺎﻝ: ﺭﺏ
ﻭﻣﺎﺫﺍ ﺍﻛﺘﺐ؟ ﻗﺎﻝ: ﺍﻛﺘﺐ ﻣﻘﺎﺩﻳﺮ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﺣﺘﻰ
ﺗﻘﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Na ji Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah yana cewa:
Lalle farkon abin da Allah Ya
halitta shi ne Alkalami, sannan Ya
ce da shi: Ka rubuta, to sai ya ce:
Ya Ubangijina mene ne zan
rubuta? Sai Ya ce: Ka rubuta
kaddarorin kome har Sa’ah ta
tsaya)). Intaha.
Kamar yadda kuke gani wannan
nassi ne na sahihin hadithi, to
amma kuma duk da haka sai ga
shi Aluusii ya hikaito daga Sufaye
cikin tafsirinsa mai suna Ruuhul
Ma’aanii 17/105 cewa sun ce ya zo
cikin Hadithi cewa Annabi mai tsira
da amincin Allah ya ce wa Sahabi
Jabir Dan Abdullahi :-
(( ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻧﻮﺭ ﻧﺒﻴﻚ ﻳﺎ ﺟﺎﺑﺮ.((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da
Allah Madaukakin Sarki Ya halitta
shi ne hasken Annabinka)). Intaha.
Don Allah ku duba ku ga irin yadda
Sufaye suka bar yin aiki da
ingantaccen hadithi, suka koma
suka kirkiro wani hadithin karya
suka jingina shi zuwa ga Annabi
mai tsira da amincin Allah, ta inda
kuwa za ku fahimci cewa hadithi ne
karya shi ne: Sam ba ya rubuce
cikin littattafan hadithi sanannu,
wannan shi ya sa ma a lokacin da
Sheik Muhammad Jameel Zainu
yake bayanin hadithai na karya
cikin littafinsa Mai suna: Minhaajul
Firqatin Naajiyah Wat Taa’ifatil
Mansuurah shafi na 74 ya ce:-
(( ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻮﺭ ﻧﺒﻴﻚ ﻳﺎ ﺟﺎﺑﺮ.” ﻣﻮﺿﻮﻉ((
. ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da
Allah Ya halitta shi ne hasken
Annabinka”. maudhuu’ine)). Intaha.
Haka ma Sheik Albanii ma a cikin
littafinsa Silsilatul Ahaadithis
Sahiihah 1/457 a lokacin da ya
kawo hadithin nan na 2,996 da
Imam Muslim ya ruwaito cikin
Sahihinsa watau:-
(( ﺧﻠﻘﺖ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻣﻦ ﻧﻮﺭ ﻭﺧﻠﻖ ﺍﻟﺠﺎﻥ ﻣﻦ ﻣﺎﺭﺝ
ﻣﻦ ﻧﺎﺭ، ﻭﺧﻠﻖ ﺍﺩﻡ ﻣﻤﺎ ﻭﺻﻒ ﻟﻜﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’an: ((An halicci Mala’iku daga
wani irin haske ne, sannan an
halicci Aljannu daga wani irin
harshen wuta mai launin baki-baki
ne, sannan kuma an halicci Adamu
ne daga abin da aka siffanta muku)
). Sai shi Albaanii ya ce:-
(( ﻓﻴﻪ ﺇﺷﺎﺭﺓ ﺍﻟﻰ ﺑﻄﻼﻥ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻤﺸﻬﻮﺭ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺎﺱ” :ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻮﺭ ﻧﺒﻴﻚ ﻳﺎ ﺟﺎﺑﺮ ”
ﻭ ﻧﺤﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺘﻲ ﺗﻘﻮﻝ ﺑﺎﻧﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺧﻠﻖ ﻣﻦ ﻧﻮﺭ، ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺩﻟﻴﻞ
ﻭﺍﺿﺢ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻓﻘﻂ ﻫﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺧﻠﻘﻮﺍ ﻣﻦ
ﻧﻮﺭ، ﺩﻭﻥ ﺍﺩﻡ ﻭﺑﻨﻴﻪ، ﻓﺘﻨﺒﻪ ﻭﻻ ﺗﻜﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻐﺎﻓﻠﻴﻦ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Cikin wannan hadithin
akwai isharar cewa hadithin nan da
ya shahara cikin harsunan mutane,
watau: “Ya Jabir farkon abin da
Allah Ya halitta shi ne hasken
annabinka” da ma irinsa daga cikin
hadithan da suke cewa: Annabi
mai tsira da amincin Allah an
halicce shi ne daga wani irin haske
magana ce ta karya. Lalle wannan
hadithin hujja ce karara da ke
nuna cewa: lalle Mala’iku ne kadai
aka halitta su daga wani irin haske,
amma banda Adamu da ‘ya’yan
shi. Sai ka fadaka, kada ka
kasance daga cikin gafalallu)).
Intaha.
Allah Ya shiryar da sufayenmu
cikin wannan Al’ummah, da ma
dukkan sauran karkatattu da ake
da su cikin wannan Al’ummah
Muhammadiyyah.
Ya Allah! Ka nuna mana gaskiya
gaskiya ce Ka ba mu ikon bin ta,
Ka nuna mana karya karya ce Ka
ba mu ikon guje mata. Ameen.
Leave a Reply