Ana so musulmi ya yawaita addu’a ranar juma’a, domin akwai lokaci da idan mutum ya dace dashi, toh Allah zai karɓi addu’ar sa. Kamar yadda aka Rawaito daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
عن أبي هُرَيرَة رَضِيَ اللهُ عنه، أنَّ رسولَ الله صلَّى اللهُ عليه وسلَّم: ((ذَكَرَ يومَ الجُمُعةِ فقال: فيه ساعةٌ لا يُوافِقُها عبدٌ مسلمٌ وهو قائمٌ يُصلِّي يسألُ اللهَ شيئًا إلَّا أعطاه إيَّاه، وأشار بيدِه يُقلِّلها))
Bukhari 935
Muslim 852
Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace annabi yace: akwai wani lokaci a ranar juma’a, babu wani Bawa musulmi da zai dace da wannan lokaci yana tsaye yana sallah yana roƙon Allah wani abu face Allah ya bashi abinda yake nema.
A wata riwaya kuma Annabi yace:
إنَّ في الجمُعة سَاعةً لا يسألُ اللهَ العبد فيها شيئًا إلاَّ آتاه اللهُ إيَاه
Akwai wani lokaci a ranar juma’a babu wani bawa da zai roƙi Allah wani abu acikin wannan lokacin face ya bashi abinda ya roƙa.
Wani lokaci ne wannan lokaci?
An samu tsaɓani tsakanin maluma kan fayyace wannan lokacin amma wanda yafi kusa da daidai sune zance biyu,
- Lokacin zaman liman har a kammala sallah, kamar yadda muslim ya rawaito.
- Bayan sallan la’asar:
Imam Ahmad ya rawaito acikin musnad ɗinsa daga Abu Sa’eed da Abu Huraira Manzon Allah yana cewa:
إنَ في الجمعة ساعةً لا يُوافِقها عَبْدٌ مسلم يَسأَلُ الله فيهَا خَيْرًا إِلاَّ أعْطاه إيَّاهُ وهِيَ بَعْدَ العَصر
Akwai wani lokaci a ranar juma’a, babu wani musulmi da zai dace da ita ya na roƙon Allah wani alheri face Allah ya bashi abinda yake nema, lokacin shine bayan sallar la’asar.
A ranar juma’a kamar yadda akeso a yawaita wa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati, toh haka kuma anaso mutum ya yawaita addu’a. Ba dole sai acikin sallah ba, kamar yadda sauran riwayar da muka kawo a baya suka nuna. Sannan kuma a sani cewa salati ga Annabi yana daga cikin abubuwa masu sanya Allah ya karɓi addu’a.
Ƴan’uwa sai mu zage dantse, mu rinƙa amfani da irin wa’innan damammaki da Allah yake bamu domin kai kukanmu gaba gareshi. Allah ya biya mana buƙatunmu baki ɗaya.
Leave a Reply