Aisha Matar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Allah ya ƙara mata yarda ta tambayi Annabi Sallallahu alaihi Wasallama game da Annoba. Sai yace mata
Annoba azaba ce wacce Allah ke sauƙar wa akan wanda yaso, sai Allah ya sanya ta ta zamto rahama ga muminai, babu wani bawa da annoba zata auka dashi, ya zauna a garinshi yana mai haƙuri da kuma neman lada a wurin Allah, yana mai tabbatar da cewa babu wani abinda zai sameshi sai abinda Allah ya rubuta masa face yana da lada kaman na shahidi.
Sahihul Bukhari: 5734
Acikin wannan hadisi annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana bayani ne kan sauƙar annoba, Allah yana sauƙar wa ne akan bayinsa, musulmai ko kafirai, amma ita wannnan annoba tana kasance wa Ni’ima ce ga bayinsa muminai, domin shi mumini lamuransa baki ɗaya alheri ne kamar yadda Annabi ya bada labari a wani hadisi, idan alheri ya sameshi sai ya gode wa Allah, sai ya sami ƙari ya kuma sami lada, haka nan in sharri ya sameshi yayi haƙuri sai Allah ya bashi ladan haƙurin da yayi.
Sannan Annabi ya nuna cewa wanda irin wannan Annoba suka sauƙa akansa yayi haƙuri, bai kiɗime ya mance da Allah ba, kaman yanda yake faruwa yanzu, da zarar irin wannan abubuwa sun faru sai a fara yaɗa jita jita da ƙarerayi, mutane duk su mance Allah. To a irin wannan hali ana so musulmi ya natsu ya maida lamuransa baki ɗaya zuwa ga Allah, ya sani cewa babu wani ahinda zai sameshi sai abinda Allah ya ƙaddara masa, in yayi haka to ya kuɓuta, in Allah yasa wannan annoba itace ajalinsa toh zai sami ladan shahidi
Abubuwan lura a wannan hadisi:
- Annoba daga Allah take, domin uƙuba ga bayinsa masu saɓa masa, ko kuma dun jarabawa.
- Annoba tana iya sauƙa kan Musulmi ko kafiri
- In annoba ta sauka a gari ba’a son mutanen garin su fice, haka nan ba’a son wa’inda suke waje su shigo, domin hakan zai taimaka wurin ƙara yaɗuwar annobar
- A lokacin Annoba anaso musulmi ya dogara ga Allah, kada ya kiɗime
- Idan Annoba ta zama sanadin Musulmi to yana da ladan shahidi.
Leave a Reply