Wannan ƙa’ida ce mai matuƙar Muhimmanci da ya wajaba akan kowani Musulmi ya fahimce shi.
الأصل في العبادة التوقف
Asali acikin harkan Ibada shine kamewa da dakatawa kada Mutum ya aikata wani Abu sai da dalili.
Wannan Shine abinda yake sananne a shari’ar Musulunci domin idan akace anbar harkar addini kowa ya kawo abinda yaga ya dace da son ranshi to haƙiƙa Hakan zai gurɓata addini ta yadda za’a kasa banbance wa tsaƙanin abinda Annabi yazo dashi da abinda mutane suka ƙirƙira.
Wasu sukan ce ai Hujja shine Annabi ya hana ba wai Annabi baiyi ba
To wannan a hankalce ko babu nassi za’a iya ruguza wannan magana tasu, domin idan har mukayi riƙo da wannan ƙa’ida da suka kawo to zai ruguza tsarin Addinin Musulunci baki ɗayan sa.
Misali Annabi ya koyar da Sallar Asubahi Raka’a biyu amma kuma babu inda yace kada a ƙara da Nassi ƙarara to anan zamu iya cewa toh zamu ƙara ta ta zama raka’a biyar sabida ai Annabi bai hana ba kuma ai Sallah aikin alheri ne.
Haƙiƙa ko masu kawo wannan ƙa’ida na tabbatar bazasu amince da hakan ba amma a haƙiƙa duk wanda ya fahimci ƙa’idar su zai fahimci cewa abinda take nufi kenan.
Kuma amfani da wannan ƙa’ida zai jawo ƙirƙirar bid’oi wanda basu da iyaka, domin kowa zai iya ƙirƙirar tashi kalar ibadar ya kuma kafa Hujja da cewa ai Annabi bai hana ba.
Saboda haka wannan ƙa’ida kuskure ce kuma babu wani daga cikin Maluma da duniyar Musulunci ta yarda dasu da ya taɓa kawo irin wannan ƙa’idar. Ƙa’ida wanda yake sananne shine Cewa “Asali a ibada shine dakatawa har sai ansamu dalili da yake umarni dashi” wannan kuma shine Ayoyi da hadisai suke mara wa baya. Domin an turo Annabi ne saboda ya koya wa mutane yadda zasu bauta wa Allah, idan ya zama cewa kowa zai iya ƙirƙirar ibada da yaga dama kuma a karɓa masa ya zama babu amfanin turo Annabi kenan. Allah yasa mudace.
Leave a Reply