Mai rubutu: Hamza Diso
Ba laifi bane mu dauki abubuwan da zasuyi mana amfani a cikin hanyoyin gudanar da rayuwar sauran Al’ummomi
A bangaren ilimi muyi aiki da wani bangare na pragmatism, ya zamo zamu maida hankali ne kawai akan abubuwan da za suyi mana Amfani a duniya ko Lahira ko duka biyun, duk wani ilimi da ba zai taimaka mana wajen Samun Yardar Ubangiji ba, ba kuma zai taimaka mana wajen samarwa Al’umma rayuwa mai kyau a duniya ba, to mu ajiye shi har sai mun gama da wadanda sukafi amfani.
Ba duk wani nau’i na ilimi da mukaji labari a wani guri zamu bashi muhimmanci ba, A’a zamu fara ne da wadanda mukafi bukata. Idan mukayi haka kaga mun amfana da bangare mai amfani na pragmatism da realism, ba tare da mun dakko bangaren da zai ci karo da yanayin mu ko al’adarmu ko Addinin mu ba.
Haka kuma a yayin da muke fama da tsarin capitalism ba laifi bane muyi amfani da wani bangare kadan na communism da socialism, muyi kokarin takaita karfin capitalists, ba tare da mun cutar dasu ba, sannan muyi kokarin raba arzikin kasa ga yan kasa gwargwadon yadda gwamnati bazata cutu ba, idan mukayi haka zamu wayi gari talaka yana iya samun dan abinda zai rage zafi, sannan kuma kowa yana da damar yin aiki tukuru ya samarwa kansa jarin da zai iya sauya masa tsarin rayuwa.
Kaga mu bamu kashe zuciyar mutanan gari ba,sannan kuma bamu maida su bayin ‘yan jari hujja ba. Sannan yan kasa zasu gani a kasa cewar dukiyar kasa tasuce dukkanin su, bata yan siyasa ba, ba kuma ta ogan ‘yan siyasa bace, wannan Wanda yake zaune a kujera yana sakace da tsinke
Leave a Reply