WASAN KWALLO!!!(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

WASAN KWALLO!!!
Sharia ta halattawa musulmi motsa
jiki don kula da lafiyar sa, da baiwa
jiki da kwakwalwa karin lafiya da
walwala. Kuma aka tsara mana
hanyoyin motsa jiki cikin kamala
da koyon jarunta don kare kai, da
samun karin kuzari da azamar
neman halal.
Yana da kyau kowa yana kulawa
da kansa da motsa gabobi, ta
hanyar aiki, ko gudu a cikin
mutumci, ko yin iyo a cikin ruwa, ko
koyon harbi, ko tsere a dawakai, ko
duk wani motsa jiki da zai kara
wartsakar da jiki cikin mutumci da
kamun kai.
Kwatsam sai ga BALL wadda aka
shardanta mata sanya gajeren
wando, katti suna ta gudun bin
wani abi cikin tsiraici, ana ta ihu, ga
haduwar maza da mata, ana busa
usur da sauran kayan bushe bushe
na shaidanci, a dauki dukkan
lokacin ka har sama da awa guda
ba tasbihi ko tilawa ko salatin
Annabi saw, bayan an tashi a
barka da labarin ta na sati guda
kana ta musu ta bacin rai da ‘yan
uwa, kuma an barka da son wanda
baka sanshi ba, wani ma son
wanda ba musulmi ba, matasa an
cusa masu shagala da son duniya
ta labarin ball. In baka dace ba ka
samu damuwa da bacin rai, ko kayi
murna mai yawa duk ba’a hanyar
Allah ba. Ko ka samu iyaye da ‘ya
‘yan su a club dabam dabam ana
ta musu ba girmama juna,
hukumomi da attajira nata batar da
kudi ta hanyar da ba samun yardar
Allah, har ana ganin laifin wanda
yace don mi ake yi?
Duk wannan hanyoyi ne na batawa
musulmi lokacin sa mai tsada, da
hanashi amfanan kan sa
musamman a lokatai masu amfani,
ga kuma cusawa yan zamani
kyamar tarbiyyar addini da motsa
jiki na halal…..
Kai abubuwan da yawa, pls yan
uwa ku taya ni. Amma a karshe ina
tambaya wacce riba musulmi ke
samu ne…?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates