Addinin Musulunci addini ne mai tsari, wanda babu wani addini ko kuma tsari na ɗan Adam a ban ƙasa da ya kaishi, wurin baiwa kowa ƴanci, da kuma sanya abubuwa yadda suka dace. Addinin musulunci ba kawai ya taƙaita a ibadah bane, ya shafi mu’amala da kuma yanayin rayuwa baki ɗaya.
A yau zamuyi magana ne kan Hukuncin Roƙo da bara a Addinin Musulunci.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance tun yana ƙarami Allah ya tarbiyanceshi kan dogaro da kai, ta yadda ya kasance yana yiwa mutanen Makkah kiwo suna biyanshi. Da abinda suke biyanshi yake gudanar da harkokin sa na yau da kullum.
Haka nan shima lokacin da Allah ya turo shi a matsayin Manzon sa zuwa ga duniya baki ɗaya, ya kasance yana tarbiyyantar sahabbansa kan dogaro da kai. Ta yadda ya kasance yana karɓan mubaya’an Sahabbansa kan cewa bazasu tambayi mutane komai ba. Har ya kai ga wani daga cikinsu sandarsa zata faɗi daga kan dabbansa amma bazai nemi wani dake ƙasa ya miƙa masa ba, sai dai ya sauka ya ɗauka da kansa, sabida cika wannan mubaya’a da yayi wa Manzon Allah. Haka halin Annabi yake, sannan kuma haka ya tarbiyyanci sahabbansa.
Thauban Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito hadisi daga Annabi yana cewa:
من يكفل لي أن لا يسأل الناس شيئاً وأتكفل له بالجنة، فقال ثوبان: أنا، فكان لا يسأل أحداً شيئاً
Abu Dawud: 1643
Manzon Allah yace:
Waye zai lamunce min kan cewa bazai tambayi mutane komai ba, ni kuma na lamunce masa Aljannah? Sai Sauban yace: Ni. Bayan wannan magana Sauban ya kasance baya tambayar mutane komai.
Hukuncin Roƙon bayan mutum na da shi:
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
من سأل الناس أموالهم تكثرًا، فإنما يسأل جمرًا؛ فليستقل أو ليستكثر
Muslim: 1041
Wanda ya tambayi mutane dukiyarsu domin ya ƙara nashi dukiyar, toh yana tambayar garwashi ne, ya rage ko kuma ya ƙara
Muslim ya rawaito hadisi na 1041
Ma’ana ya rage wannan garwashi ko kuma ya ƙara yawanta, duk dai babu mafita, mafita shine kamewa ga barin roƙon. Kuma wannan ne yake nuna cewa roƙo alhali mutum yana da wadata Yana daga cikin manƴan laifuka da kan kai ga mutum shiga wuta.
Meye hukuncin roƙo idan mutum yana da buƙata?
Addinin Musulunci bai hana roƙo baki dayansa ba, A’a yayi hanine kan roƙon da bai zama dole ba, kaman mutum yaƙi fita neman abinda zai rufa asirinsa, sai yaje ya rinƙa roƙon mutane, ko kuma mutumin da yana dashi amma sai yaje yana roƙon mutane, wannan sune Addini yayi hani akansu. Amma inya zamto mutum bashi da yadda zaiyi, kuma gashi yana da buƙata, toh babu laifi yayi roƙo domin samun fita daga matsalar da yake ciki. Kuma daga zarar ya fita daga matsalar toh shikenan sai ya kame ga barin roƙo.
Abu Hamid Algazali yace:
Asali roko haramun ne, yana halatta ne kawai sabida lalura, ko kuma buƙata mai tsanani, domin acikin roƙo akwai kai koken Allah zuwa ga bayinsa, da kuma nuna rashin yalwatar ni’imar Allah akan bawansa, akwai kuma ƙasƙantar da kai wanda shi mai roƙon zaiyi zuwa ga wanda ba Allah ba, kuma sau da dama roƙo baya rabuwa da cutar da wanda aka roƙa, wani lokaci kodai ya bayar domin kunya, ko kuma domin riyaa.
Ihya’u ulumiddeen: 4/223
Annabi yayi bayanin mutanen da Roƙo ya halatta a garesu kaman haka:
إنَّ المَسْأَلَةَ لا تَحِلُّ إلَّا لأَحَدِ ثَلاثَةٍ: رَجُلٍ تَحَمَّلَ حَمالَةً، فَحَلَّتْ له المَسْأَلَةُ حتَّى يُصِيبَها، ثُمَّ يُمْسِكُ، ورَجُلٌ أصابَتْهُ جائِحَةٌ اجْتاحَتْ مالَهُ، فَحَلَّتْ له المَسْأَلَةُ حتَّى يُصِيبَ قِوامًا مِن عَيْشٍ، أوْ قالَ: سِدادًا مِن عَيْشٍ، ورَجُلٌ أصابَتْهُ فاقَةٌ حتَّى يَقُومَ ثَلاثَةٌ مِن ذَوِي الحِجا مِن قَوْمِهِ: لقَدْ أصابَتْ فُلانًا فاقَةٌ، فَحَلَّتْ له المَسْأَلَةُ حتَّى يُصِيبَ قِوامًا مِن عَيْشٍ، أوْ قالَ سِدادًا مِن عَيْشٍ، فَما سِواهُنَّ مِنَ المَسْأَلَةِ يا قَبِيصَةُ سُحْتًا يَأْكُلُها صاحِبُها سُحْتًا.
Muslim: 1044
Sahabin Annabi Qabeesat Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi cewa:
Roƙo bata halatta sai ga ɗaya daga cikin ukun nan:
1. Wanda ya ɗauki lamani(kaman ya sami wasu suna rikici kan dukiya, sai yace zai biya domin ya kashe wutan rikicin) to wannan ya halatta masa ya roƙi ƴan’uwa musulmi domin sauƙar da wannan nauyi dake kansa
2. Wanda wata musiba ko annoba ta afka masa( kamar wacce gobara ta cinye masa shago, ko kuma gona ko makamantansu) shima ya halatta yayi roƙo domin neman abinda zaici idan bashi dashi.
3. Wanda talauci ta kama shi, har aka samu mutane uku daga cikin masu hankali da tunani suka tabbatar da cewa wane yana cikin talauci. Toh shima wannan ya halatta a gareshi yayi roƙo domin samun abinda zai rufa asirinsa, da zarar ya samu sai ya kame.
Sai Annabi yace: duk wani mai roƙo bayan wa’innan toh Haramun yake karɓa, Haramun!
Muslim ya rawaito: 1044
kunga yadda addinin Musulunci yake tarbiyyantar Mabiyansa, koda mutum ya zamto ya halatta masa yayi roƙo toh akwai iyaka. Bawai mutum ya mayar dashi sana’a ba.
Da kayi roƙo gwara kaje kayo itace a daji kazo ka siyar:
Sahabi Zubai bn Awwam ya rawaito hadisi daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace:
لأن يأخُذَ أحدُكم حَبْلَهُ، فيأتي بحِزْمَةِ الحَطَب على ظهره، فيبيعها، فيَكْفِ الله بها وجهَه – خيرٌ له من أن يسأل الناس، أعطَوْهُ أو منعوه
Bukhari: 1471
ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya taho da dami na itace a bayansa ya siyar, domin sama wa kansa rufin asiri yafi masa alheri kan ya tambayi mutane, su bashi ko su hanashi
Bukhari ya rawaito: 1472. Wannan sharhi ne ba tarjama ba.
Roƙo yana ƙara talauci:
Abu kabshata Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi yace:
Bawa bazai buɗe ƙofar tambayar mutane ba face Allah ya buɗe masa kofar talauci.
Sunan at-tirmidi: 2325
Shiyasa mai roƙo zaka ganshi kullum sai ƙara talauci yake, sabida abinda yake samu bashi da albarka. Kullun a cikin talauci.
Allah ya kyauta. Ya rabamu da roƙo, ya mana buɗi ya kuma bamu ikon neman na kai.
Leave a Reply