Addinin Musulunci a koda yaushe yana kokari wurin dakile duk wata tsabani da rashin jituwa tsakanin Mabiyansa, shiyasa a wurare da dama Allah da Manzonsa suka hana mu yin tsabani da rarrabuwa kamar yadda Allah yace:
Kuyi Biyayya ga Allah da Manzonsa, kada kuyi jayayya sai kusamu rauni, sannan karfin ku ya tafi.
Suratul Anfal Ayah: 46
Sabida Hakane ma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya hana Mutum musulmi yayi nema kan neman dan’uwansa Musulmi. Annabi Sallallahu Alaihi wasallama yace:
Kada mutum yayi nema akan neman dan’uwansa
Bukhari: 5144
Muslim: 1413
Wannan Hadisi a bayyane yake cewa haramun ne mutum yasan cewa Dan’uwansa Musulmi yana neman auren wata, kuma iyayenta da ita sun amsa mishi sa’annan kuma yaje shima ya shiga nemanta. Sai dai idan bata amsa mishi ba, toh anan zai iya zuwa ya nema har sai ta tsayar da wadda takeso a tsakaninsu.
Abin Lura: Idan har ya zamto bata amince da wanda ya fara zuwa wurinta ba to ya halatta ga na biyun yaje ya nemi aurenta,
Haka nan idan shi na farkon ne ya janye ko kuma yayi izini wa na biyun yaje ya neme ta to anan babu laifi.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply