BAYANI A KAN MAULIDI KASHI NA BIYU (ii) (Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

SHUBUHOHIN DA MASU BUKIN
MAULIDI KE KAFA HUJJA DA SU A
KAN BUKIN MAULIDI DA SUKE YI:
Asabar 3/3/1435 H 4/1/2014 M
Yan’uwa Musulmi! Akwai shubuhohin
da masu bukin maulidi ke ambatawa
a gaban wadanda suka raina wa
hankali da karatu a matsayin hujjojin
da suke wajabta yin bukin maulidi ko
suke halatta shi, saboda haka Ina
sha Allah Ta’ala za mu ambaci uku
daga cikinsu a wannan rubutu namu
(kashi na biyu ii) sannan mu ba da
amsarsu mu yi musu raddi, saboda
burin da muke da shi na tsarkake
addinin Musulunci daga wannan
bidi’ah mai kama da bidi’ar Kirsimeti
wacce Kiristoci ke yi cikin ko wace
shekara.
****************************
SHUBUHA TA FARKO:
Shubuha ta farko: Suka ce: Allah ne
da kansa Ya yi umurni da yin bukin
maulidi cikin Suratu Yunus aya ta 58
a inda ya ce:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ
ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Ma’ana: {Ka ce: Ku yi farin ciki da
falalar Allah da rahamarSa shi ne
mafi alheri daga abin da suke
tarawa}.
Sai masu bidi’ar maulidi suka ce:
Annabi shi ne falalar Allah da
rahamarSa, Allah kuwa Ya ce a yi
farin ciki da falalarSa da kuma
rahamarSa, farin cikin kuwa yana
nufin shirya bukin maulidinsa ne ahi
Annabi mai tsira da amincin Allah, ke
nan shirya bukin maulidi ko wace
shekara bin wani umurni ne na
musamman Wanda ya fito daga Allah
madaukakin Sarki, rashin bin wannan
umurni kuwa lalle saba wa Shi Allah
Madaukakin Sarki ne!!!
Amsa a kan wannan shubuha ta yan
bidi’ar maulidi tana da rassa da
yawa:-
Na farko: sai a ce da su: Fassara
wannan ayar da cewa tana umurni ne
da yin bukin maulidi fassara ce da
take Kama da fassarar Baatiniyyah da
gulaatus suufiyyah da suke yi wa
wasu nassoshin Alkur’ani mai girma,
kamar yadda suka fassara ayah ta 25
cikin Suratu Nuuhin inda Allah Yake
magana game da mutanen Annabi
Nuhu Ya ce:-
{ ﻣﻤﺎ ﺧﻄﻴﺌﺎﺗﻬﻢ ﺃﻏﺮﻗﻮﺍ ﻓﺄﺩﺧﻠﻮﺍ ﻧﺎﺭﺍ ﻓﻠﻢ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻟﻬﻢ
ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻧﺼﺎﺭﺍ }.
Ma’ana: {Saboda laifukansu na
ganganci aka nitsar da su (cikin
ruwa) sannan aka sanya su a Wuta.
Saboda haka ba su sama wa kansu
wanin Allah a matsayin Mai taimako
ba}.
Sai suka ce: ma’anar ayar ita ce:
Allah Yana nufin cewa abin nan da
suka yi wa Annabi Nuhu na saba wa
umurnin da Allah ya aiko shi da shi
shi ne ya Kai su ga yin nitso cikin
tekunan sanin Allah! Watau dai abin
nan da suka yi na saba wa Annabi
Nuhu babu wani zunubi a cikinsa
kamar yadda wasu ke tsammani!!
Suka kuma fassara inda Allah Ya ce
cikin Suratul Israa’i aya ta 23:-
{ ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺇﻳﺎﻩ }.
Ma’ana: {UbangijinKa Ya hukunta
cewa kada ku bauta wa kowa sai
Shi}.
Sai suka ce: Ma’anar ayar ita ce:
“Ubangijinka Ya riga ya kaddara
muku cewa ba za ku yi wata bauta ba
face Allahn ne dai kuka bautawa!
saboda haka babu wani abu a
duniyan da za ku bautawa face a
hakikanin lamari Allah ne Shi
kadanSa kuka bautawa!!
Suka kuma fassara inda Allah ya ce
cikin Suratul Hijri aya ta 99 :-
{ ﻭﺍﻋﺒﺪ ﺭﺑﻚ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻴﻚ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ }.
Ma’ana: {Kuma ka bauta wa
Ubangijinka har mutuwa ta zo maka}.
Sai suka ce: ma’anarsa shi ne: shi
Dan Adam ana umurtansa da yin
ibada ne har zuwa lokacin da ya kai
matsayin Yakini da sanin Allah, da
zarar ya kai wannan matsayi ayyukan
ibada sun fadi ke nan a Kansa!!
Reshe na biyu: Sai a ce da su: Wani
malami ne cikin maluman tafsiiri
daga magabata Salafus Salih ya
fassara wannan ayar da irin wannan
fassara taku ta cewa: Ana nufin yin
bukin maulidi ne da wannan ayah?
Lalle muna tabbatar wa masu karatun
wannan rubutu namu cewa: har
abada yan bidi’ar maulidi ba za su
iya kawo koda malamin tafsiiri daya
ba daga cikin Salafus Salih da ya
fassara wannan ayar da cewa tana
nufin umurni ne da yin bukin maulidi.
Rashe na uku: Sai a ce wa masu
bidi’ar maulidi: In dai har wannan
ayar tana nufin yin bukin maulidi ne
to kuwa lazimin hakan shi ne:
Sahabbai da sauran shugabannin
Al’ummah kamar su Abu Hanifah, da
Mali, da Shafi’ii da Ahmad, da
sauransu dukkansu ke nan sun nuna
kiyayya da rashin kauna ga Manzon
Allah Mai tsira da amincin Allah,
sannan dukkansu ke nan sun saba
wa umurnin Allah da ya zo cikin
wannan aya ta 58 da ta zo cikin
Suratu Yunus, domin har suka gama
rayuwarsu babu wani daga cikinsu
da ya taba yin bukin maulidi! Duk
kuwa wanda ya ce: Sahabbai, da
Taabi’ai da sauran shugabannin
Al’ummah ba sa kaunar Manzon Allah
ko ba sa girmama shi, ba sa bin
umurnin Allah da ya zo cikin
Alkur’ani na girmama shi to lalle
wannan ya bace bata bayyananniya!
Lazimin wannan kuwa shi ne: Yan
bukin maulidi su ne batattu saboda
lazimin maganarsu ta tabbatar da
cewa Sahabban Manzon Allah da
Taabi’ai, da Taabi’utttaabi’ina da
sauran Sugabannin Al’ummah batattu
ne, saboda ba su yi aiki da wannan
aya ba:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ
ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Reshe na hudu: Sai a ce da Yan
maulidi: Dukkan abin da bai zama
nuna soyayya ba ne ga Manzon Allah
a zamanin Shabbai da Taabi’ai da
sauran Shugabanni kamar Imam
Malik, da Abu Hanifah, da Shaa’i’ii, da
Ahmad, to ba zai zama nuna soyayya
ga Manzon Allah ba a wannan
zamani namu.
Idan kuma wani daga cikin yan bukin
maulidi ya fidda jahilcinsa a fili ya
ce: Ai Suyuutii ya halatta yin bukin
maulidi ! Sai a ce da shi: Ai shi
Suyuutii ba ya daga cikin wadanda
ake kira Magabata cikin Musulunci,
a’a yana cikin jerin yan baya ne,
domin ya mutu ne a shekara ta 911
na hijira watau yau shekara 523 ke
nan da suka wuce. Kuma shi Suyuutii
a wurin Malamai mutum ne da yake
kama da mai tara kirare cikin dare, ya
kan dauki kirare sannan ya kan dauki
macizai da kunamu, saboda wannan
idan har ya halatta bidi’ar bukin
maulidi ba wani abin mamaki ba ne a
gurin Malamai, domin ya yi ma abin
da ya fi hakan muni da ban mamaki,
saboda Mai littafin Rimaahu Hizbir
Rahiim ya ce a cikin wannan littafi
nasa wanda aka buga tare da littafin
Jawaahirul Ma’aa’nii 1/199 ya ce shi
Suyuutii ya ce cikin littafinsa mai
suna :-
ﺗﻨﻮﻳﺮ ﺍﻟﺤﻠﻚ ﻓﻲ ﺇﻣﻜﺎﻥ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ
“Ya ga Annabi kuma ya yi taro da shi
a farke har sau saba’in da wani abu”!
Mai irin wannan magana mara tushe
don ya ce bukin maulidi halal ne
mene abin mamaki a cikin
maganarsa? Allah Ya tsare daga
fadawa cikin ko wace irin halaka.
Ameen.
SHUBUHA TA BIYU:
Shubuha ta biyu suka ce: Duk wata
ni’ima da Allah Ya yi wa mutum, to
dole ne ya gode aw Allah a kanta,
saboda lokacin da Annabi ya dawo
Madinah ya ga Yahudawa suna azumi
a ranar goma ga watan Muharram sai
shi Annabi mai tsira da amincin Allah
ya tambaye su ya ce: Me ya sa kuke
azumin wannan rana? Sai suka ce
masa: Wannan rana ce da Allah Ya
tsirar da Annabi Musa tare da
jama’arsa, kuma Ya halakar da
Fir’auna tare da mutanensa cikin
teku, shi ya sa Annabi Musa yake
azumin wannan rana saboda gode wa
Allah mu ma shi ya sa muke yin
azuminsa, sai Annabi mai tsira da
amincin Allah Ya ce: Mun fi ku
cancantar yin abin da Annabi Musa
ya yi, saboda haka ya yi azumin
wannan ranar kuma ya umurci
Musulmi da su yi azuminsa. A nan
muna ganin babu wata ni’ima da ta
kai haihuwar Annabi Muhammad mai
tsira da amincin Allah, kuma ko
shakka babu wannan ni’ima za ta
wajabta mana gode aw Allah, wannan
kuwa shi ya sa muke yin bukin
maulidi saboda nuna godiya ga Allah
Madaukakin Sarki.
Amsa a kan wannan shubuha tasu
sai a ce da su: Lalle gaskiya ne
ni’imomin Allah suna wajabta godiyar
Allah a kan bayinSa, to amma hakika
ni’ima mafi girma a cikin Musulunci
ita ce:Ni’imar ba wa Annabi mai tsira
da amincin Allah Manzanci, ba. Wai
ni’imar haihuwar sa ba, domin
Alkur’ani mai girma bai yi nuni da
ishara zuwa haihuwarsa koda sau
daya ba, to amma ya yi nuni da
ishara zuwa ga manzancinsa ba sau
daya ba ba sau biyu ba! Allahl
Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu
Aa’li Imraan aya ta 164:-
{ ﻟﻘﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺑﻌﺚ ﻓﻴﻬﻢ ﺭﺳﻮﻻ
ﻣﻦ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﺘﻠﻮ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﻭﻳﺰﻛﻴﻬﻢ ﻭﻳﻌﻠﻤﻬﻢ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ }.
Ma’ana: {Hakika Allah Ya yi babbar
falala ga muminai domin Ya aika da
Manzo daga ainihinsu yana karanta
musu ayoyinSa Yana tsarkake su
yana karantar da su Littafi da Hikima}
. A nan Allah bai ce: domin an haifi
wani Manzo daga cikinsu ba, a’a sai
Ya ce: Domin an aiko wani manzo.
Wannan shi ne halin da za ku tarar
game da ko wane Manzo daga cikin
manzannin Allah Madaukakin Sarki,
watau abin himmantuwa game da shi
shi ne aiko shi ba wai ranar
haihuwarsa ba, kamar dai yadda
Allah Madaukakin Sarki ya ce cikin
Suratul Bakara aya ta 213:-
{ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻣﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻓﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﺒﺸﺮﻳﻦ
ﻭﻣﻨﺬﺭﻳﻦ ﻭﺍﻧﺰﻝ ﻣﻌﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻟﻴﺤﻜﻢ ﺑﻴﻦ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻓﻴﻪ }.
Ma’ana: {A da mutane sun kasance
al’umm ce guda daya, sai Allah Ya
aiko Annabawa suna masu bishara
suna masu gargadi, kuma Ya saukar
da Littafi da gaskiya tare da su’
domin ya yi hukunci tsakanin mutane
cikin abin da suka Saba aw juna
cikinsa}. Kun gani a nan’ da dai
mayar da wata rana Idi da sunan
addini halal ne cikin addinin
Musulunci, to da kuwa marar da aka
aiko Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah Idi shi ne ya fi.
Sannan kuma game da azumin da shi
Annabi mai tsira da amincin Allah ya
yi na ranar Aashuuraaa to fa dole ne
mu sani cewa: Shi fa Annabi mai
tsira da amincin Allah shi ne mai
shar’antawa kuma mai isar da sako
daga Ubangijinsa zuwa ga sauran
mutane, saboda haka ba ya halatta a
gare mu mu yi kiyasin wani mutum a
kan shi, har na mu fada cikin wata
bidi’a, domin abin da ake bukata ga
dukkan al’ummar Musulmi shi ne: Su
zama masu bi a koda yaushe ba wai
masu kirkiro bidi’o’i ba. Sannan kuma
shi azumi ai kishiyar bukin Idi ne
saboda azumi yana nufin hana sa kai
cin abinci shi kuwa bukin Idi yana
nufin ciyar da kai abinci ne, saboda
haka ta kaka za a kira yin azumi
bukin Idi?
SHUBUHA TA UKU:
Shubuha ta uku: suka ce: Annabi mai
tsira da amincin Allah ya kasance
yana azumi a ko wane ran litinin, a
lokacin da Sahabbai suka tambaye
shi: Don me yake azumi a wannan
rana? Sai ya ce: yana azumtar ko
wace litinin ne saboda a ran litinin
ne aka haife shi.
Yan maulidi suka ce wannan yana
nufin ke nan Annabi mai tsira da
amincin Allah shi ma yana bukin
maulidi watau yana bukin ranar
haihuwarsa.
Amsa a kan wannan shubuha ta yan
maulidi sai a ce da su:-
Na daya: Musulmi ba sa musun
halaccin azumin ranar litinin da kuma
falalarsa, haka ma azumin ranar
alhamis da falalarsa, to amma shi
wannan azumin aka yi shi ne cikin
dukkan kwanakin litinin da alhamis
na shekara, ba wai sau daya ne ba
kawai ake yin shi cikin shekara,
kamar yadda masu yin bidi’ar maulidi
suke yin shi sau daya cikin shekara.
Na biyu: lalle kiyasta bukin maulidi a
kan azumin ranar litinin da ake yi
cikin ko wane mako, kiyasin abin da
yake bidi’ah ne a kan bin da yake
Sunnah, wannan kuwa Kiyasi ne
batacce.
Na uku: lalle inda su masu bukin
maulidi suna son koyi ne da Annabi
mai tsira da amincin Allah cikin abin
da shi Annabin ya yi a ranar
haihuwarsa, to da sai su wadatu da
abin da shi Annabi mai tsira da
amincin Allah ya wadatu da shi,
watau sai su rika yin azumi cikin ko
wace ranar litinin, ba wai su rika
bukin maulidi cikin ko wace ranar
gama sha biyu ga watan Rabi’ul
Awwal ba, saboda shi Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah bai yi
maulidi a ranar goma sha biyu ga
watan Rabi’ul Awwal ba duk kuwa da
cewa yana damar yin hakan in da yin
hakan ya dace da Shari’ar Musulunci,
to amma da yake hakan bai dace da
Shari’ar Musulunci sam bai yi hakan
ba, abin kawai aka sani ya yi shi ne:
Azumin ranar litinin cikin ko wane
mako. Ke nan wannan zai wajabta wa
yan bukin maulidi in har dai suna
son Annabi suna kuma girmama shi
suna kaunar bin hanyar da ya bi, su
bar yin bukin maulidi a ranar goma
sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal su
koma yin azumin ranar litinin ko
wane mako, da kuma ranar alhamis
ko wane mako.
Wannan shi ne karshen bayaninmu a
kan bukin maulidi cikin wannan kashi
na biyu, za mu ci gaba da bayanin
shubuhohin masu yin maulidi da
kuma yin raddi a kan wadnnan
shubuhohin a bayaninmu cikin kashi
na uku (iii) in sha Allahu Ta’ala.
Manufarmu da wannan rubutu namu
shi ne a gudu tare a tsira tare,
Musulmi su tsarkake addininsu daga
dukkan wata bidi’ah su rika gina
lamuran addininsu a kan hujja watau
Alkur’ani da Sunnah.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki
Ya taimake mu Ya nuna mana
gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin
ta, Ya nuna mana karya karya karya
ce Ya ba mu ikon kin ta. Ameen

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “BAYANI A KAN MAULIDI KASHI NA BIYU (ii) (Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. […] BAYANI A KAN MAULIDI KASHI NABIYU (ii) (Ibrahim Jalo Jalingo). […]

  2. Muhammad Avatar
    Muhammad

    Lallai iska na walalda mai kayan kara,abun naka babu komai sai son rai da karya da hassada tareda juya ma’anar magana. wlh abun naka dariya yabani sosai WAI amatsayinka na Dr amma Haryanzu kakasa gane yadda addini yake……Mtssssss.

Leave a Reply

Categories
Latest updates