BAYANI A KAN MAULIDI KASHI
NA BIYU (ii)
SHUBUHOHIN DA MASU BUKIN
MAULIDI KE KAFA HUJJA DA SU
A KAN BUKIN MAULIDI DA SUKE
YI:
Yan’uwa Musulmi! Akwai
shubuhohin da masu bukin maulidi
ke ambatawa a gaban wadanda
suka raina wa hankali da karatu a
matsayin hujjojin da suke wajabta
yin bukin maulidi ko suke halatta
shi, saboda haka Ina sha Allah
Ta’ala za mu ambaci uku daga
cikinsu a wannan rubutu namu
(kashi na biyu ii) sannan mu ba da
amsarsu mu yi musu raddi, saboda
burin da muke da shi na tsarkake
addinin Musulunci daga wannan
bidi’ah mai kama da bidi’ar
Kirsimeti wacce Kiristoci ke yi cikin
ko wace shekara.
Shubuha ta farko: Suka ce: Allah
ne da kansa Ya yi umurni da yin
bukin maulidi cikin Suratu Yunus
aya ta 58 a inda ya ce:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ
ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ}.
Ma’ana: {Ka ce: Ku yi farin ciki da
falalar Allah da rahamarSa shi ne
mafi alheri daga abin da suke
tarawa}.
Sai masu bidi’ar maulidi suka ce:
Annabi shi ne falalar Allah da
rahamarSa, Allah kuwa Ya ce a yi
farin ciki da falalarSa da kuma
rahamarSa, farin cikin kuwa yana
nufin shirya bukin maulidinsa ne
ahi Annabi mai tsira da amincin
Allah, ke nan shirya bukin maulidi
ko wace shekara bin wani umurni
ne na musamman Wanda ya fito
daga Allah madaukakin Sarki,
rashin bin wannan umurni kuwa
lalle saba wa Shi Allah
Madaukakin Sarki ne!!!
Amsa a kan wannan shubuha ta
yan bidi’ar maulidi tana da rassa
da yawa:-
Na farko: sai a ce da su: Fassara
wannan ayar da cewa tana umurni
ne da yin bukin maulidi fassara ce
da take Kama da fassarar
Baatiniyyah da gulaatus suufiyyah
da suke yi wa wasu nassoshin
Alkur’ani mai girma, kamar yadda
suka fassara ayah ta 25 cikin
Suratu Nuuhin inda Allah Yake
magana game da mutanen Annabi
Nuhu Ya ce:-
{ ﻣﻤﺎ ﺧﻄﻴﺌﺎﺗﻬﻢ ﺃﻏﺮﻗﻮﺍ ﻓﺄﺩﺧﻠﻮﺍ ﻧﺎﺭﺍ ﻓﻠﻢ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻟﻬﻢ
ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻧﺼﺎﺭﺍ}.
Ma’ana: {Saboda laifukansu na
ganganci aka nitsar da su (cikin
ruwa) sannan aka sanya su a
Wuta. Saboda haka ba su sama
wa kansu wanin Allah a matsayin
Mai taimako ba}.
Sai suka ce: ma’anar ayar ita ce:
Allah Yana nufin cewa abin nan da
suka yi wa Annabi Nuhu na saba
wa umurnin da Allah ya aiko shi da
shi shi ne ya Kai su ga yin nitso
cikin tekunan sanin Allah! Watau
dai abin nan da suka yi na saba wa
Annabi Nuhu babu wani zunubi a
cikinsa kamar yadda wasu ke
tsammani!!
Suka kuma fassara inda Allah Ya
ce cikin Suratul Israa’i aya ta 23:-
{ ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺇﻳﺎﻩ}.
Ma’ana: {UbangijinKa Ya hukunta
cewa kada ku bauta wa kowa sai
Shi}.
Sai suka ce: Ma’anar ayar ita ce:
“Ubangijinka Ya riga ya kaddara
muku cewa ba za ku yi wata bauta
ba face Allahn ne dai kuka
bautawa! saboda haka babu wani
abu a duniyan da za ku bautawa
face a hakikanin lamari Allah ne
Shi kadanSa kuka bautawa!!
Suka kuma fassara inda Allah ya
ce cikin Suratul Hijri aya ta 99 :-
{ ﻭﺍﻋﺒﺪ ﺭﺑﻚ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻴﻚ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ}.
Ma’ana: {Kuma ka bauta wa
Ubangijinka har mutuwa ta zo
maka}. Sai suka ce: ma’anarsa shi
ne: shi Dan Adam ana umurtansa
da yin ibada ne har zuwa lokacin
da ya kai matsayin Yakini da sanin
Allah, da zarar ya kai wannan
matsayi ayyukan ibada sun fadi ke
nan a Kansa!!
Reshe na biyu: Sai a ce da su:
Wani malami ne cikin maluman
tafsiiri daga magabata Salafus
Salih ya fassara wannan ayar da
irin wannan fassara taku ta cewa:
Ana nufin yin bukin maulidi ne da
wannan ayah? Lalle muna tabbatar
wa masu karatun wannan rubutu
namu cewa: har abada yan bidi’ar
maulidi ba za su iya kawo koda
malamin tafsiiri daya ba daga cikin
Salafus Salih da ya fassara
wannan ayar da cewa tana nufin
umurni ne da yin bukin maulidi.
Rashe na uku: Sai a ce wa masu
bidi’ar maulidi: In dai har wannan
ayar tana nufin yin bukin maulidi
ne to kuwa lazimin hakan shi ne:
Sahabbai da sauran shugabannin
Al’ummah kamar su Abu Hanifah,
da Mali, da Shafi’ii da Ahmad, da
sauransu dukkansu ke nan sun
nuna kiyayya da rashin kauna ga
Manzon Allah Mai tsira da amincin
Allah, sannan dukkansu ke nan
sun saba wa umurnin Allah da ya
zo cikin wannan aya ta 58 da ta zo
cikin Suratu Yunus, domin har
suka gama rayuwarsu babu wani
daga cikinsu da ya taba yin bukin
maulidi! Duk kuwa wanda ya ce:
Sahabbai, da Taabi’ai da sauran
shugabannin Al’ummah ba sa
kaunar Manzon Allah ko ba sa
girmama shi, ba sa bin umurnin
Allah da ya zo cikin Alkur’ani na
girmama shi to lalle wannan ya
bace bata bayyananniya! Lazimin
wannan kuwa shi ne: Yan bukin
maulidi su ne batattu saboda
lazimin maganarsu ta tabbatar da
cewa Sahabban Manzon Allah da
Taabi’ai, da Taabi’utttaabi’ina da
sauran Sugabannin Al’ummah
batattu ne, saboda ba su yi aiki da
wannan aya ba:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ
ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ}.
Reshe na hudu: Sai a ce da Yan
maulidi: Dukkan abin da bai zama
nuna soyayya ba ne ga Manzon
Allah a zamanin Shabbai da
Taabi’ai da sauran Shugabanni
kamar Imam Malik, da Abu
Hanifah, da Shaa’i’ii, da Ahmad, to
ba zai zama nuna soyayya ga
Manzon Allah ba a wannan zamani
namu.
Idan kuma wani daga cikin yan
bukin maulidi ya fidda jahilcinsa a
fili ya ce: Ai Suyuutii ya halatta yin
bukin maulidi ! Sai a ce da shi: Ai
shi Suyuutii ba ya daga cikin
wadanda ake kira Magabata cikin
Musulunci, a’a yana cikin jerin yan
baya ne, domin ya mutu ne a
shekara ta 911 na hijira watau yau
shekara 523 ke nan da suka wuce.
Kuma shi Suyuutii a wurin Malamai
mutum ne da yake kama da mai
tara kirare cikin dare, ya kan dauki
kirare sannan ya kan dauki macizai
da kunamu, saboda wannan idan
har ya halatta bidi’ar bukin maulidi
ba wani abin mamaki ba ne a gurin
Malamai, domin ya yi ma abin da
ya fi hakan muni da ban mamaki,
saboda Mai littafin Rimaahu Hizbir
Rahiim ya ce a cikin wannan littafi
nasa wanda aka buga tare da
littafin Jawaahirul Ma’aa’nii 1/199
ya ce shi Suyuutii ya ce cikin
littafinsa mai suna :-
ﺗﻨﻮﻳﺮ ﺍﻟﺤﻠﻚ ﻓﻲ ﺇﻣﻜﺎﻥ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ
“Ya ga Annabi kuma ya yi taro da
shi a farke har sau saba’in da wani
abu”! Mai irin wannan magana
mara tushe don ya ce bukin
maulidi halal ne mene abin
mamaki a cikin maganarsa? Allah
Ya tsare daga fadawa cikin ko
wace irin halaka. Ameen.
Shubuha ta biyu suka ce: Duk wata
ni’ima da Allah Ya yi wa mutum, to
dole ne ya gode aw Allah a kanta,
saboda lokacin da Annabi ya dawo
Madinah ya ga Yahudawa suna
azumi a ranar goma ga watan
Muharram sai shi Annabi mai tsira
da amincin Allah ya tambaye su ya
ce: Me ya sa kuke azumin wannan
rana? Sai suka ce masa: Wannan
rana ce da Allah Ya tsirar da
Annabi Musa tare da jama’arsa,
kuma Ya halakar da Fir’auna tare
da mutanensa cikin teku, shi ya sa
Annabi Musa yake azumin wannan
rana saboda gode wa Allah mu ma
shi ya sa muke yin azuminsa, sai
Annabi mai tsira da amincin Allah
Ya ce: Mun fi ku cancantar yin abin
da Annabi Musa ya yi, saboda
haka ya yi azumin wannan ranar
kuma ya umurci Musulmi da su yi
azuminsa. A nan muna ganin babu
wata ni’ima da ta kai haihuwar
Annabi Muhammad mai tsira da
amincin Allah, kuma ko shakka
babu wannan ni’ima za ta wajabta
mana gode aw Allah, wannan
kuwa shi ya sa muke yin bukin
maulidi saboda nuna godiya ga
Allah Madaukakin Sarki.
Amsa a kan wannan shubuha tasu
sai a ce da su: Lalle gaskiya ne
ni’imomin Allah suna wajabta
godiyar Allah a kan bayinSa, to
amma hakika ni’ima mafi girma a
cikin Musulunci ita ce:Ni’imar ba
wa Annabi mai tsira da amincin
Allah Manzanci, ba. Wai ni’imar
haihuwar sa ba, domin Alkur’ani
mai girma bai yi nuni da ishara
zuwa haihuwarsa koda sau daya
ba, to amma ya yi nuni da ishara
zuwa ga manzancinsa ba sau daya
ba ba sau biyu ba! Allahl
Madaukakin Sarki Ya ce cikin
Suratu Aa’li Imraan aya ta 164:-
{ ﻟﻘﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺑﻌﺚ ﻓﻴﻬﻢ ﺭﺳﻮﻻ
ﻣﻦ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﺘﻠﻮ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﻭﻳﺰﻛﻴﻬﻢ ﻭﻳﻌﻠﻤﻬﻢ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ }.
Ma’ana: {Hakika Allah Ya yi babbar
falala ga muminai domin Ya aika
da Manzo daga ainihinsu yana
karanta musu ayoyinSa Yana
tsarkake su yana karantar da su
Littafi da Hikima}. A nan Allah bai
ce: domin an haifi wani Manzo
daga cikinsu ba, a’a sai Ya ce:
Domin an aiko wani manzo.
Wannan shi ne halin da za ku tarar
game da ko wane Manzo daga
cikin manzannin Allah Madaukakin
Sarki, watau abin himmantuwa
game da shi shi ne aiko shi ba wai
ranar haihuwarsa ba, kamar dai
yadda Allah Madaukakin Sarki ya
ce cikin Suratul Bakara aya ta
213:-
{ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻣﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻓﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﺒﺸﺮﻳﻦ
ﻭﻣﻨﺬﺭﻳﻦ ﻭﺍﻧﺰﻝ ﻣﻌﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻟﻴﺤﻜﻢ ﺑﻴﻦ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻓﻴﻪ }.
Ma’ana: {A da mutane sun kasance
al’umm ce guda daya, sai Allah Ya
aiko Annabawa suna masu bishara
suna masu gargadi, kuma Ya
saukar da Littafi da gaskiya tare da
su’ domin ya yi hukunci tsakanin
mutane cikin abin da suka Saba
aw juna cikinsa}. Kun gani a nan’
da dai mayar da wata rana Idi da
sunan addini halal ne cikin addinin
Musulunci, to da kuwa marar da
aka aiko Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah Idi shi ne ya fi.
Sannan kuma game da azumin da
shi Annabi mai tsira da amincin
Allah ya yi na ranar Aashuuraaa to
fa dole ne mu sani cewa: Shi fa
Annabi mai tsira da amincin Allah
shi ne mai shar’antawa kuma mai
isar da sako daga Ubangijinsa
zuwa ga sauran mutane, saboda
haka ba ya halatta a gare mu mu yi
kiyasin wani mutum a kan shi, har
na mu fada cikin wata bidi’a, domin
abin da ake bukata ga dukkan
al’ummar Musulmi shi ne: Su zama
masu bi a koda yaushe ba wai
masu kirkiro bidi’o’i ba. Sannan
kuma shi azumi ai kishiyar bukin Idi
ne saboda azumi yana nufin hana
sa kai cin abinci shi kuwa bukin Idi
yana nufin ciyar da kai abinci ne,
saboda haka ta kaka za a kira yin
azumi bukin Idi?
Shubuha ta uku: suka ce: Annabi
mai tsira da amincin Allah ya
kasance yana azumi a ko wane ran
litinin, a lokacin da Sahabbai suka
tambaye shi: Don me yake azumi a
wannan rana? Sai ya ce: yana
azumtar ko wace litinin ne saboda
a ran litinin ne aka haife shi.
Yan maulidi suka ce wannan yana
nufin ke nan Annabi mai tsira da
amincin Allah shi ma yana bukin
maulidi watau yana bukin ranar
haihuwarsa.
Amsa a kan wannan shubuha ta
yan maulidi sai a ce da su:-
Na daya: Musulmi ba sa musun
halaccin azumin ranar litinin da
kuma falalarsa, haka ma azumin
ranar alhamis da falalarsa, to
amma shi wannan azumin aka yi
shi ne cikin dukkan kwanakin litinin
da alhamis na shekara, ba wai sau
daya ne ba kawai ake yin shi cikin
shekara, kamar yadda masu yin
bidi’ar maulidi suke yin shi sau
daya cikin shekara.
Na biyu: lalle kiyasta bukin maulidi
a kan azumin ranar litinin da ake yi
cikin ko wane mako, kiyasin abin
da yake bidi’ah ne a kan bin da
yake Sunnah, wannan kuwa Kiyasi
ne batacce.
Na uku: lalle inda su masu bukin
maulidi suna son koyi ne da
Annabi mai tsira da amincin Allah
cikin abin da shi Annabin ya yi a
ranar haihuwarsa, to da sai su
wadatu da abin da shi Annabi mai
tsira da amincin Allah ya wadatu
da shi, watau sai su rika yin azumi
cikin ko wace ranar litinin, ba wai
su rika bukin maulidi cikin ko wace
ranar gama sha biyu ga watan
Rabi’ul Awwal ba, saboda shi
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah bai yi maulidi a ranar goma
sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal
ba duk kuwa da cewa yana damar
yin hakan in da yin hakan ya dace
da Shari’ar Musulunci, to amma da
yake hakan bai dace da Shari’ar
Musulunci sam bai yi hakan ba,
abin kawai aka sani ya yi shi ne:
Azumin ranar litinin cikin ko wane
mako. Ke nan wannan zai wajabta
wa yan bukin maulidi in har dai
suna son Annabi suna kuma
girmama shi suna kaunar bin
hanyar da ya bi, su bar yin bukin
maulidi a ranar goma sha biyu ga
watan Rabi’ul Awwal su koma yin
azumin ranar litinin ko wane mako,
da kuma ranar alhamis ko wane
mako.
Wannan shi ne karshen
bayaninmu a kan bukin maulidi
cikin wannan kashi na biyu, za mu
ci gaba da bayanin shubuhohin
masu yin maulidi da kuma yin raddi
a kan wadnnan shubuhohin a
bayaninmu cikin kashi na uku (iii)
in sha Allahu Ta’ala.
Manufarmu da wannan rubutu
namu shi ne a gudu tare a tsira
tare, Musulmi su tsarkake
addininsu daga dukkan wata
bidi’ah su rika gina lamuran
addininsu a kan hujja watau
Alkur’ani da Sunnah.
Muna rokon Allah Madaukakin
Sarki Ya taimake mu Ya nuna
mana gaskiya gaskiya ce Ya ba
mu ikon bin ta, Ya nuna mana
karya karya karya ce Ya ba mu
ikon kin ta. Ameen.
Leave a Reply