Assalamu Alaikum ƴan Uwa Musulmi.
Haƙiƙa wannan kisan Gilla da kuma cin Amana da akayi wa ɗan’uwa Sheikh Goni Aisami abune mai matuƙar baƙanta rai, ace Jami’in tsaro da ya kamata ya baiwa mutum kariya shine kuma zai yi irin wannan aiki. Allah ya kyauta.
Amma abinda yafi ja min hankali shine yadda Shuwagabannin mu Musulmai da Masu faɗa aji acikinmu wanda suke gaggawar yin Allah wadai idan aka taɓa wani wanda ba Musulmi ba sukayi shiru kan wannan lamari, Musamman ma wanda ya kashe wannan ɗan uwa ba Musulmi bane, ƙaddara ace Soja ne Musulmi ya kashe Pastor shin kana ga yanzu da ƙasar nan bata ɗauki zafi ba? Bada jimawa ba muna da labarin abinda ya faru da Deborah, Yadda ƙasannan ta ɗau zafi, har shugaban ƙasa sai da yayi jaje yayi Allah wadai, Amma lokacin da aka kashe wata Mata Musulma da ƴaƴanta a ƙasar iyamurai Baka ji ƙasar ta ɗau zafi kamar yadda akayi lokacin deborah ba.
Shin da ace Soja Musulmi ne ya kashe Pastor shin sauran Kiristoci da Ƙungiyarsu ta CAN bazasu mayar da abin ya zamto ta addini ba?
kowa yasan su wanene kiristocin Nigeria da Kuma ƙungiyarsu ta CAN da rashin adalci da sukeyi wa Musulmi a koda yaushe.
ƙarin abin haushi shine yadda wasu ƴan siyasanmu suke lallaɓinsu ta yadda idan abu mai muni ya sami Musulmi basu iya fita cikin gaggawa suyi Allah wadai amma idan ya sami wanda ba Musulmi bane sai su fita cikin gaggawa suna jaje suna nuna Allah wadai, Abin yanzu ya fara kaiwa har ga Maluman Musulunci da Sarakunan gargajiya, bazakaji sautinsu ba yayin da aka taɓa mutanensu sai dai lokacin da aka taɓa wasu alokacin zaka ga sun fito suna surutu. Wannan ba ƙaramar illa bane ga wannan Al’ummah.
Shi Musulmi a kodayaushe dole ya nuna shi Musulmi ne, kuma yana alfahari da addininsa, bawai ya rinƙa kunyar bayyana addininsa ba, Hakan kuma bashi zai bashi ɗaukaka ba.
Riƙo da Addini da bin Allah shine zai kawo wa Mutum ɗaukaka bawai bijire wa Allah da biye wa mutane ba.
Yanzu ka duba ansha samun lokuta mabanbanta wanda ake kashe mana mutane a kudancin ƙasannan, Amma haka abin zaizo ya wuce ba’a wani ɗaukan Mataki akai, haka nan kuma shuwagabannin yankin da abin ya faru bazasu nuna kulawa kan lamarin ba.
Ƴan uwa lokaci yayi da zamu tashi mu kare haƙƙokinmu, mu kuma rinƙa zaɓan mutane masu kishin mu da Addinin mu, wanda basu da tsoron fitowa fili don kare mana muradin mu, haka nan lokaci yayi da zamu tashi idan akayi wani abu na cutar damu mu yaɗa shi wa duniya kowa ya sani kamar yadda suma suke yaɗa wa, sannan kuma mubi kadin Abinda akayi mana ta hanyoyin da suka dace.
Mu sani wannan duniyar da muke ciki duniya ce ta Nuna ƙarfinka aji tsoronka. Shiyasa zakuga ƙasashe manya manya kullum ƙere ƙeren makamai suke ɗaɗa yi badun komi ba domin baiwa abokan gabar su tsoro, Domin idan ɗan ta’adda yasan kana da tanadi to zai ji tsoron tinƙarar ka, amma idan yasan baka da tanadi to akowani lokaci zai iya far maka. Wannan kukan kurciya ne.
Muna roƙon Allah ya gafarta Wa Ustaz Goni yasa ya huta, Allah ya daɗa ɗaukaka Addininsa. Wassalamu Alaikum.
Leave a Reply