BAYANIN IBNU TAIMIYYAH GAME DA CIN YANKAN DA AHLUL KITABI SUKA YI SABODA IDINSU

Danna nan domin shiga karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo.
Kwanakin baya mun yi bayani gameda hukuncin karban kyautukan idi na dukkan nau’ukan kafurai, mun kuma yi bayani game da hukuncin cin yankan da Ahlul Kitabi; watau Yahudawa da Kiristoci suka yi saboda idodinsu, to amma muna jin akwai mutanen da suka karanta wancan rubutun namu amma kuma suka kasa fahimtar wani bangare nasa, watakila saboda yawan rubutun. Dalilin da ya sa kuwa muka ce akwai wadanda ba su fahimci abin da aka rubuta sosai ba shi ne: irin yadda aka cigaba da aiko mana da tambayoyi game da mas’alar cin yankan da Ahlul Kitabi suka yi domin bukuwan idodinsu.
***************
A wannan rubutu namu za mu kawo bayanan Salaf ne da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya kawo dangane da hukuncin cin yankan da Yahudawa da Kiristoci suka yi domin bukukuwan idodinsu. Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/555,558 :-
((وأما ما ذبحه اهل الكتاب لاعيادهم وما يتقربون بذبحه الى غير الله نظير ما يذبح المسلمون من هداياهم وضحاياهم متقربين بها الى الله تعالى، وذلك مثل ما يذبحون للمسيح والزهرة، فعن احمد روايتان: اشهرهما في نصوصه: انه لا يباح اكله وان لم يسم غير الله تعالى. ونقل النهي عن ذلك عن عائشة وعبد الله بن عمر…..والرواية الثانية ان ذلك مكروه غير محرم))

Ma’ana: ((To amma abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah’ kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An kuma nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A’isha, da Abdullahi Dan Umar….. Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)). 
Har yanzu Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/559 :-
((ونقلت الرخصة في ذبائح الأعياد ونحوها عن طائفة من الصحابة رضي الله عنهم، وهذا فيما اذا لم يسموا غير الله، فان سموا غير الله في عيدهم او غير عيدهم حرم في اشهر الروايتين، وهو مذهب الجمهور، وهو مذهب الفقهاء الثلاثة فيما نقله غير واحد، وهو قول علي بن ابي طالب وغيره من الصحابة، وهو قول اكثر فقهاء الشام وغيرهم. والثانية: لا يحرم وان سموا غير الله، وهذا قول عطاء ومجاهد ومكحول والاوزاعي والليث)).
Ma’ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmad yake da su a cikin mas’alar, wannan kuwa shi ne mazhabar Jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha’un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Bin Abi Taa’lib, da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Bin Saa’riyah, da Ubaa’dah Bin Saa’mit, kuma shi ne maganar malaman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa, da Mujaa’hid, da Makhuul, da Auzaa’iy, da kuma Laith)).
Allah muke roko da Ya yi mana muwafaka har kullum. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates