Cukurkuɗaɗɗun takardu 2 ( Hadisan Fiƙihu)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

By: Hamza Diso

Iliman addini da ake neman su don kansu ( wato su ba hanya bace ta sanin wani ilimin) sun kasu gida uku

  • Aƙida
  • Fiƙhu
  • Ilimin gyaran zuciya

Duka waɗannan ilimai ana samun su ne a matakin farko a cikin wahayi, wato Alƙur’ani da hadisi. Sai dai su (Alƙur’ani da hadisin) ba su kaɗai ne dalilai da ake kafa hujja dasu a Shari’a ba, don nassukansu suna da iyaka, da adadi, su kuma ayyukan bayi baza su iyakantu a wani adadi sananne ba, shiyasa aka bayar da wasu hanyoyi na gano hukuncin duk wata mas’ala da zata afko bayan yankewar wahayi

A Fiƙhu muna da nau’ikan dalilai guda biyu

  • waɗanda Jumhur suka haɗu akai
  • waɗanda akwai saɓani a kansu, ko da kuwa kusan kowa yana amfani da wasunsu a fakaice.

Kason farko sun haɗa Alƙur’ani da Hadisi da Ijma’i da ƙiyasi, kuma duk malamai sun haɗu akan su, ban da zahiriyya, kuma suma akwai mas’alolin da ake tuhumar su da yin ƙiyasi a cikinsu, (cewa nayi tuhuma), sannan akwai mas’aloli da suke da alaka da ƙur’ani da hadisi da ake da saɓani akansu, kamar babin umarni da hani, shin umarni yana hukuntar da wajibci kai tsaye? Ko istihbabi? Sannan shin yana fa’idarta da maimaici ko kuma a’a, shin ƙira’a shaza ana iya kafa hujja da ita idan tana da isnadi sahihi? Shin Ittisali sharaɗi ne a ingancin hadisi ko a iya aiki da hadisi Mursal?…. Misali ne kawai.

Haka shima Ijma’i akwai wasu mas’aloli a ƙarƙashinsa da akayi saɓani akansu, shima ƙiyasi haka.

Ɓangare na biyu na dalilai suma akwai saɓani akan su, ba don kada maganar tayi tsaho ba da na hakaito wani abu a ciki, amma wataran zamu tattauna.

To su hadisan fiƙihu a ina ake samun su? Amsar wani tana da sauƙi sosai, kasan malaman hadisi sun yi rubuce rubuce kala-kala, cikin nau’ikan littattafan da suka rubuta akwai masu suna “السنن” su waɗannan littattafai ana tattara iya hadisan fiƙihu ne a cikinsu kawai, kuma mafi girmansu shine Assunanul kubra السنن الكبرى na Imam Albaihaƙi, sannan Assunan na Abu Dawud (waɗannan littattafai sun amsa sunansu sosai, kuma littafin Albaihaƙi babban kundi ne da ya tattare kusan duk abinda zaka nema) da Aljami’u na Imam Attirmizi (ƙwarai ya cancanci a kirashi da Aljami’u ba sunan ba) shi littafin Tirmizi yana da muhimmanci wajen sanin mazhabobin malamai da hadisan da aiki ya wakana akansu. da sauran littattafai masu ɗauke da wannan sunan, sannan Almusannaf na Ibnu abi shaibah, da kuma na Abdurrazzaƙ,su Almusannafat sune litattafan da suke tattara fatawoyin Sahabbai da ma tabi’ai da kuma tsarma hadisin Annabi. Sannan ga Muwaɗɗa da sauransu.

Akwai littattafai da suke tattare dalilan wata Mazhaba a hadisan ce, kamar mudawwana wacce ta ƙunshi kusan Hadisai dubu huɗu (4000) waɗannan hadisan kuma Imamu Suhnun yana ruwaito su ne ta hanyar Ibnu Wahab a cikin Muwaɗɗarsa ( lura, muwaɗɗa ce mai zaman kanta ba ruwaito ta yayi daga Maliku ba, shiyasa zaka ga yana ruwaito hadisai a cikinta ta hanyar wasu malaman nasa, kamar Laisu ɗan Sa’ad da Ibnu Lahi’ah) Mudawwana babban kundi ne da zamu ware masu batu mai zaman kansa a wani lokacin, don itace babban littafin Malikiyya kuma ana gabatar da ita akan Muwaɗɗa a rajihi, sannan ga Attamhid na Ibnu Abdilbarr, ga littafin Al’ahkamul wusɗa na Imam Abdulhaƙ Al’ishbili, wanda akansa ne aka rubuta littafinالوهم والإيهام ba dan ina tattaunawa ne ta mahangar fiƙhu ba da nayi magana akan waɗannan littattafai guda biyu, sannan ga sharhunan da Malikawa sukayiwa Bukhari da Muslim da Tirmizi da ma wasu cikin litattafan hadisi waɗanda zaka sami bayanai dayawa akan dalilansu a hadisance.

To amma idan ka samu hadisin ka na fiƙihu a ina zaka sami hukunci akan inganci ko rashin ingancinsa? Mu haɗu a rubutu na gaba

Aci naman Sallah lafiya

Leave a Reply

Latest updates
Categories