An rawaito Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance yana ɗaga hanunsa sama yayi Addu’a, sannan ɗaga hannu Sama yayin Addu’a yana daga cikin sabuban karɓar Addu’a. Domin Allah yana kunyar bawansa ya ɗaga hannayensa sama ya roƙe shi kuma ya dawo da hannayensa ba tare da ya amsa masa ba, kamar yadda aka rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama(Ahmad 23715).
Batun shafan fuska da hannaye kuma ansamu tsaɓani tsaƙanin Maluma kan ingancin yin hakan.
Amma batu mafi inganci shine hakan bai inganta ba.
Magabata da dama sun nuna rashin ingancin hakan.
Imam Ibn taimiyyah yace:
Amma ɗaga hannaye sama yayin Addu’a an rawaito Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana yinsa, kuma hadisai ingatattu sunzo akan haka, amma game da shafan fuska bayan Addu’a ba’a samu wasu hadisai ba sai wa’inda basu wuce ɗaya zuwa biyu ba, wanda kuma basu da ƙarfin da za’a kafa hujja dasu.
Majmu’ul Fatawa: 22/519
An tambayi Sheikh Bin Uthaymeen game da shafar fuska bayan Addu’a sai yace:
Shafan fuska bayan Addu’a abinda yafi kusa da gaskiya shine ba’a shar’anta hakan ba, domin hadisan da aka rawaito kan haka hadisai ne masu rauni, har Sheikhul Islam yace hujja bazata kafu dasu ba.
Idan har bamu tabbatar ba, ko kuma muka samu zato mai yawa cewa wannan abu Shari’a ne toh abinda yafi dacewa shine barinsa, domin shi Shari’a baya tabbata da zato kawai sai dai in ya zamto zato ne gamamme.
Abinda nake gani shine shafar fuska bayan Addu’a ba sunna bace. abune sananne cewa Annabi yayi Addu’a a hudɗubar Juma’a domin neman ruwan sama, ya ɗaga hannayensa sama, amma ba’a rawaito cewa ya shafi fuskarsa dasu ba. Hakanan kuma wasu hadisai da sukazo daga Annabi game da Addu’a da yayi ya ɗaga hannayensa sama amma ba’a rawaito ya shafi fuskarsa dasu ba,
Majmu’u Fatawa ibn Uthaymeen: 14/781
Da haka za’a fahimci cewa abinda yafi dacewa shine mutum yayin Addu’a ya ɗaga hannayensa sama bayan ya kammala sai ya dawo dasu ba tare da shafa fuskarsa ba. Allah yasa mudace.
Leave a Reply