Muslim ya rawaito hadisi Acikin Sahihinsa. Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) yace:
من صلى صلاة الصبح فهو في ذمة الله، فلا يطلبنكم الله من ذمته بشيء، فإنه من يطلبه من ذمته بشيء يدركه، ثم يكبه في نار جهنم .
Abinda Hadisin yake bayani a Jumlace shine: Duk wanda yayi sallan Asubahi. Ana nufin yayi ta a lokacin ta, kuma acikin Jam’i in ya zamto yana daga cikin wa’inda Jam’i ta hau kansu kuma bashi da wani uzuri. Toh yana ƙarƙashin kulawar Allah da Amincin sa. Kada ku yadda ku cutar dashi har Allah ya kamaku da laifin kun cutar da wanda ke ƙarƙashin Amincinsa da Kulawarsa. Domin duk wanda yayi haka Allah zai kamashi kuma ya kifar dashi a wuta.
Wannan hadisin yana daga cikin hadisan da suke nuna Falalar sallan Asubahi. Da kuma girmanta, domin babu mai kiyayeta sai mai ƙarfin imani, kuma itace sallah da tafi nauyi akan munafukai, da ita da Sallar Isha’i, ba kowa yake iya kiyayeta ba. Kuma da mutane sun san falalarta da koda da ja da ciki zasuje suyi ta.
Yana daga cikin Falalar sallan Asubahi da sallar Isha’i, An rawaito Hadisi daga Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
من صلى العشاء في جماعة كمن قام نصف الليل، ومن صلى الصبح في جماعة كمن قام الليل كله
Duk wanda ya sallaci Isha’i cikin Jama’a kaman wanda ya sallaci rabin dare ne, haka nan duk wanda ya sallaci sallar Asubahi acikin Jam’i kaman wanda ya sallaci dare ne baki ɗaya.
Irin wannan babban falala babu wata sallah da ta sami irinta, sai ayi ƙoƙari a kiyaye sallah, domin Sallah itace ganuwa tsakanin mutum da ko wani irin Sharri, tana Hana mutum Tsaɓo, tana kare mutum daga musibu da yawa, ranan tashin Alqiyama ita Allah zai fara sakamako akanta, idan tayi kyau toh Bawa ya tsira, idan kuma aka samu akasi toh Bawa kada ya zargi kowa face kansa. Allah yasa mudace. Wasallamu Alaikum.
Leave a Reply