Mai rubutu: Hamza Diso
Fahimtar sirrin da yake cikin hada sunaye guda biyu na Allah a jere a guri guda yana taimakawa wajen Kara Sanin Allah da kuma kara fahimtar Aya.
misali; fadin Allah madaukaki
وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُوا أَيْدِيَهُمَا جَزَاءً بِمَا كَسَبَا نَكَالًا مِنَ اللَّهِ وَاللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ فَمَنْ تَابَ مِنْ بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ
Ayar farko ta ‘kare da sunaye guda biyu wato Al’aziz ( mabuwayi mai cikakkiyar izzar da ba tawaya a cikin ta) da kuma Alhakim ( mai cikakkiyar hikima Wanda baya hukunci ba tare da manufa ba, kuma Wanda yake sa komai a inda ya dace)
Idan ka hada sunayen guda biyu zaka fahimci cewa izzar Allah akwai hikmah a cikinta kamar yadda hikimar sa ma akwai izza aciki, shiyasa aka hada su guri guda, wato buwayar sa ba kawai buwaya ce Mara manufa ba, kamar yadda hikimar sa akwai izza da isa acikin ta.
Sannan idan ka sake kallon Ayar zaka ga lallai wadannan sunaye sune sukafi cancanta a rufe ayar dasu, kamar Allah yana cewa: ya buwaya ya isa ya dau mataki akan duk Wanda ya sabawa umarnin sa, shiyasa yace a yanke masa (barawo) hannu tun da ya sabawa hanin da Allah yayi masa yana sane, kuma Allah yayi wannan hukunci ne cikin cikakkiyar hikimar da babu irinta, Allah ba so yake a yanke hannayen mutane ba, sai dai cikin hikimar sa yasan cewa idan aka zartar da wannan hukuncin akan mutane kadan to kowa zai shiga taitayin sa ko dan ya tsira da hannun sa, kaga ta haka dukiyar mutane zata kubuta kuma suma barayin zasu samawa Kansu Sana’a, kenan hukuncin ya zamo maslaha ga ‘barawo da mai kaya dukkan su.
Aya ta biyu Allah ya rufe ta da sunayen Algafur da Arraheem ( mai cikakkiyar gafara da jin kai) don ya nunawa barawo cewa fa ba kinsa ake yi ba, ba kuma so akeyi ya zauna cikin mummunan hali ba, don haka ya tuba ya dawo ga Allah kofa a bude take.
Haka idan ka kalli karshen ayar da tayi magana akan ‘yan fashi da makamantan su, bayan Allah ya bawa Alkali zabi akan hukuncin daya fi dacewa da kowanne dan fashi gwargwadon girman laifin sa kodai a kashe shi ko a Kore shi daga gari (wasu suna cewa a ‘daure shi) ko kuma a yanke masa hannu da ‘kafa..
Sai Allah yace: duk Wanda ya tuba (ya mika wuya) kafin Ku samu iko a kanshi (Ku kama shi) to kusan cewa lallai Allah yana da yawan gafara da jin kai.
Wato Ku sassauta masa a hukunci kuji ‘kansa sai dai idan shima ya kashe mutane to a wannan lokaci sai aga me ya dace dashi.
Wato har ‘dan fashi Allah baso yake a kama shi a kashe ba, Allah yafi son ya tuba ya zama mutumin kirki sama da a kama shi ayi maganin sa
Lallai rahamar Allah da jin kansa da soyayyar sa ga bayin sa suna da yawan gaske, Allah ka samu cikin bayin ka na gari
Leave a Reply