Mai rubutu: Hamza Diso
1. kuskure na iya jefa Al’umma cikin bala’i
Yayin da Annabi yunus yayi da’awa mutane sukaƙi amsawa, sai Azabar Allah ta tunkaro su.
Jefawa mutane tsoro da halakar dasu idan zunubi yayi yawa ba bakon abu bane a tarihi, bari na bada misali guda biyu
- Mutanan saba’a: Daular saba’a daula ce mai karfin gaske da tarihi mai tsaho ga arziki ta ko ina, Wannan daula an Santa tun kafin Shekara ta 1100 kafin haihuwar Annabi Isa, wato Sama da shekara 3000 kenan daga yau, Allah ya siffanta mana yadda yayi musu yalwa da kuma yadda yayi musu ukuba da laifin su yayi yawa, Allah yace
لَقَدْ كَانَ لِسَبَإٍۢ فِى مَسْكَنِهِمْ ءَايَةٌ ۖ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٍۢ وَشِمَالٍۢ ۖ كُلُواْ مِن رِّزْقِ رَبِّكُمْ وَٱشْكُرُواْ لَهُۥ ۚ بَلْدَةٌ طَيِّبَةٌ وَرَبٌّ غَفُورٌ
سورة السبإ : ١٥
Lallai Akwai abun lura ga mutanan Saba’a (sunan kakansu ne) game da (yadda muka tsara) garinsu, ga Lambuna a hagu da daman (Wanda zai shigo garin su), (Sai muka ce musu) “kuci daga cikin Arzikin mahaliccin Ku, kuma Ku gode masa(ta hanyar yi masa biyayya) gari mai dadi (ba kwari ba abubuwa masu cutarwa) ga kuma mahalicci mai yawan gafara.
Surat-Saba: 15
Ba Wannan ce kawai ni’imar da akayi musu ba, tsallake aya daya zaka ga Allah yace:
وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ ٱلْقُرَى ٱلَّتِى بَٰرَكْنَا فِيهَا قُرًى ظَٰهِرَةً وَقَدَّرْنَا فِيهَا ٱلسَّيْرَ ۖ سِيرُواْ فِيهَا لَيَالِىَ وَأَيَّامًا ءَامِنِينَ
السبإ:١٨
Muka sanya garuruwa tsakanin su da garin da mukayiwa Albarka (wato sham) muka takaita Nisan da yake tsakanin su( ta yadda idan zasu tafi sham kasuwanci basa bukatar daukar guziri don garu-ruwa basa yankewa akan hanya, suna barin gari zasu tarar da wani garin)
Surat-Saba: 18
Mai makon su godewa Allah suyi masa da’a su kyautata abinda yake tsakanin su da Allah, sai suka bijire ( kamar yadda muke a yanzu dukkanin mu, Allah ya yafe mana) Allah yace:
فَأَعْرَضُواْ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ سَيْلَ ٱلْعَرِمِ وَبَدَّلْنَٰهُم بِجَنَّتَيْهِمْ جَنَّتَيْنِ ذَوَاتَىْ أُكُلٍ خَمْطٍۢ وَأَثْلٍۢ وَشَىْءٍۢ مِّن سِدْرٍۢ قَلِيلٍۢ
السبإ: ١٦
Sai suka kau da kai (ga shariyar mu) sai muka tura musu maimakon ruwan tafkin su( ruwan ya cinye gidaje da dukiyoyi yayi barna mai yawan gaske) kuma muka sauya musu lambunansu da wasu masu abinci kadan da kuma bishiyoyi masu ɗaci da kuma dan itacen (Tamarisk, ina barar sunansa da Hausa) da kuma magarya ‘yar kadan.
Allah yace:
السبإ: ١٧
ذَٰلِكَ جَزَيْنَٰهُم بِمَا كَفَرُواْ ۖ وَهَلْ نُجَٰزِىٓ إِلَّا ٱلْكَفُورَ
Haka muka saka musu akan kafircin su, yo dama akwai Wanda mukewa irin wannan sakamakon idan ba (mutum) mai yawan kafirci ba…!!??
Surat-Saba: 17
- Misali na biyu mutanan Makkah: Allah yace:
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ ءَامِنَةً مُّطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِّن كُلِّ مَكَانٍۢ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ ٱللَّهِ فَأَذَٰقَهَا ٱللَّهُ لِبَاسَ ٱلْجُوعِ وَٱلْخَوْفِ بِمَا كَانُواْ يَصْنَعُونَ
النحل: ١١٢
Allah ya buga misali da wata Alkarya(Makkah) wadda ta kasance cikin Aminci da nutsuwa, Abinci yana zuwar musu ta ko ina, sai suka kafircewa ni’imomin Allah, sai Allah ya dan-dana musu yunwa da tsoro saboda abinda suke aikatawa.
Annahl: 112
Saboda tsabar yunwar da aka jarrabesu da ita har hayaki suke gani a Sama idan sun daga Kansu
Allah yace:
فَٱرْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِى ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٍۢ مُّبِين()ٍۢ يَغْشَى النَّاسَ هَذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ ()رَبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُون
الدخان: ١٠
Kayi dakon ranar da sama zatazo da hayaki mabayyani, zai lullub’e mutane (har su dinga cewa) wannan Azaba ce mai radadi, Mahaliccinmu ka yaye mana Azaba mu muminai ne.
Addukhan: 10
Har zuwa fadin Allah:
َ إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلا إِنَّكُمْ عَائِدُونَ
يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَى إِنَّا مُنتَقِمُون
الدخان: ١٥-١٦
Zamu yaye muku azabar kadan, kuma tabbas zaku koma cikin laifi(mun sani), ranar da zamu yi kamu, babban kamu, lallai mu masu daukar fansa ne (zamu kama Ku a gaba, yana nufin ranar da za ayi yakin badar)
Addukhan: 15-16
Abun nufin dai shine zunubi yana kawo ukuba, to sai dai ita wannan ukuba idan ta saukarwa wannan Al’umma to zata Debi rabonta ne ta tafi amma baza ta karar damu ba.
2. fa’ida ta biyu; tuba yana zama sababin yaye azaba:
Allah yace:
يونس: ٩٨
فَلَوْلَا كَانَتْ قَرْيَةٌ ءَامَنَتْ فَنَفَعَهَآ إِيمَٰنُهَآ إِلَّا قَوْمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُواْ كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ ٱلْخِزْىِ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَمَتَّعْنَٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍۢ
Babu wata Al’umma da su kayi imani (bayan ganin alamar azaba)kuma imanin yayi musu amfani sai mutanan (Annabi) yunus, sanda su kayi imani sai muka yaye musu azaba mai kaskantarwa a duniya, kuma muka jiyar dasu dadi har zuwa wani lokaci
Yunus: 98
Wato tuba yana kawar da musiba ya kawo jin dadi kamar yadda Annabi Nuhu ya fadawa mutanan sa, Allah yace:
فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّارًا (10) يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُم مِّدْرَارًا (11) وَيُمْدِدْكُم بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَل لَّكُمْ جَنَّاتٍ وَيَجْعَل لَّكُمْ أَنْهَارًا (12)
نوح: ١٠
Sai nace Ku nemi gafarar mahaliccin Ku, shi mai yawan gafara ne, (idan kunyi haka)sai ya turo muku da ruwan Sama (mai Albarka) ya kuma kara muku yalwar dukiya da ‘ya’ya, ya sanya muku lambuna da ‘koramu
Surat-Nuh: 10
3. Akan iya jarrabar babban makusancin Allah, kifi ya hadiye Annabi yunus:
4. An fi saurin amsa addu’ar mutumin da yake yiwa Allah da’a kafin musiba ta fado masa
Allah yace:
فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَ . لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعثون
سورة الصافات: ١٤٣
Badan dama can ya kasance cikin masu yawaita tasbihi ba, da ya zauna a cikin(kifin) Har ranar tashin bayi
Assaffat: 143
5. falalar zikirin Annabi yunus
Allah yace:
وَذَا النُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَاضِباً فَظَنَّ أَن لَّن نَّقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَى فِي الظُّلُمَاتِ أَن لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ * فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ الْغَمِّ وَكَذَلِكَ نُنجِي الْمُؤْمِنِينَ
الأنبياء: ٨٧
Hujjar itace fadinsa( sai muka amsa masa kuma muka tseratar dashi daga bakin ciki, Irin haka ne muke tserar da muminai.
Al-Anbiya: 87
Allah muna rokon ka da sunayanka da siffofinka da imanin mu dakai, Allah ka yaye mana damuwa da kunci da takura, ka bamu ikon sauya wadanda basu cancanta ba, kada ka barmu da iyawarmu mu masu rauni ne.
Leave a Reply