Ga kaɗan daga cikin Falalolin Suratul Baqara
- Tana korin Shaiɗan: An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: ” Shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta Suratul Baqara”
- Tana bada kariya ga mai karanta ta Ranar Tashin kiyama: An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: Ku karanta masu Haskakawannan guda biyu Baqara da Aal Emran, domin zasu zo ranar tashin Alƙiyama kamar Girgije guda biyu a siffar tsuntsaye wanda suke haɗe da juna su tsare mai karanta su, su Zamto Hujja a gareshi”
- Samun Albarka da karanta ta: An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: ” Ku karanta Suratul Baqara, Domin riƙo da ita albarka ne, barinta kuma hasara ne”
- Girmama wa da Sahabbai suke yi ga wanda ya karance ta: An rawaito daga Anas Allah ya ƙara masa yarda yace: ” Mutum ya kasance idan ya karanci Suratul Baqara da Aal Emran ana lissafa shi daga manya a cikinmu.
Wannn kaɗan kenan daga cikin falalar wannan Surah Mai Albarka, duk maison samun kariya a gidansa da Albarka sai ya lazimci karanta wannan Surah acikin gidansa.
Abinda Anas yake nufi da wanda ya karanci Surar shine: Ya Haddace, sannan ya san Ma’anar ta.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply