Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar 23-November-2019

Danna nan domin shiga karatu Online

Fatawa

Shimfida. Tsolaci akan fadin Allah {swt)


ليس بأمانيكم ولا أماني أهل الكتاب من يعمل سوءا يجز به ولا يجد له من دون الله وليا ولا نصيرا 

Tambayoyi:

  1. Idan liman uzuri ya sa shi fita daga sallah ya janyo wanda bai haddace in da yake karantawa ba, shin wanda aka janyo zai iya karanta wata Sura daban?
  2. Hukuncin sallar mace da niqabi .
  3. Shin mace zata iya fita daga gidan aurenta don hidimta ma mahaifinta da ya ke da lalura?
  4. Matsayin yaron da aka sace shi aka canza mishi addini ya mutu akan kafirci?
  5. Shin akwai rama sallah ga wanda tsananin rashin lafiya ya sa shi sambatu ko gushewar hankali?
  6. Ya inganta Allah ne ya daura auren Nana Fatima da Sayyidi Ali dakanShi?
  7. Wanda ya dinga sace kudin mahaifiyan shi, yaya zai yi ya kubuta bayan ya girma, yayi nadama?
  8. Hukuncin mace mai diban abinda mijinta ya kawo ta kai ma mahaifanta?
  9. Ingancin hana ba ma yara yan qasa da wata shida ruwa?
  10. Ya hallata mutum ya Karanta al-qur’ani domin isar da ladan ma matar shi da ta bar duniya!
  11. Lokacin suna ma jaririn da aka haifa kafin wata tara!
  12. Mai ya kamata ayi da abinda aka yanka domin suna.
  13. Banbancin sunna da mubah.
  14. Akwai hadisi ingantacce da yake nuna sahun gaba yafi na baya?
  15. Mutumin da yace wa matarsa in sun sake fada, sai ya sake su. Yaya matsayin aurensu bayan da suka sake fadan ya kirasu ya jaddada musu alqawarin sakin da ya musu?
  16. Hukuncin sakin da Alqali ya sa akayi?
  17. Mutumin da aka sa masa roba na fitsari saboda rashin lafiya, zai cigaba da Sallah a haka ko sai an cire roban?
  18. Ya hallata mutum yayi tsarin iyali domin tsoron talauci ko rage adadin al’uma?
  19. Matsayin hadisin da ke cewa “ saki shine mafi abin qin da Allah ya hallata”
  20. Hukuncin mutumin da yake daukan hoton haja a yanar gizo, ya tallata. In ya samu mai saya, sai ya sayo da kudin shi, ya sayar mishi!
  21. Mutumin da zai bada bashi ta hanyar ciro kudin a POS, ya hallata idan za a biya shi bashin, ya karba harda kudin “charges” da aka cire mishi a POS?
  22. Mace da take mura harda zazza6i duk lokacin da ta sa ruwa don wanke kai yayin wanka janaba ko al’ada- shin akwai wani rangwame?

Download

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar 23-November-2019”
  1. […] Archive Fatawowin Rahama 23-11-2019 Fatawowin Rahama 16-11-2019 Fatawowin Rahama 02-11-2019 Fatawowin Rahama 26-10-2019 […]

Leave a Reply

Categories
Latest updates