Shimfida: Sharhin Hadithin Abdullahi dan Abbas – Koyarwar Annabi (saw) mai tsada ga Abdullahi dan Abbas (ra).
Tambayoyin dake ciki:
- Banbancin taron suna da walima
- Ya hallata mutum ya canza sunan da iyayensa suka sa mishi zuwa sunan wani jagora?
- Mutum zai iya amfani da al-Qur’anin wani massalaci?
- Shin iyalan barawo da aka kashe shi a qoqarin kama barawon- za su iya neman diyyar kashe shi?
- Wanda ya wayi gari da janaba lokacin sanyi zai iya alola maimakon wanka domin tsoron fitar lokacin sallar asuba?
- Adduar bude sallah da ake cewa “ Allahu Akbar Kabiran wa Subhannallahi bukratan wa asilan” ya inganta?
- Ya hallata in anyi alola a shafa mai (lotion)?
- Abinda ya kamata ayi ma mamaci in an kaishi maqabarta da bayan an dawo daga maqabarta
- Akwai kaffara ga wanda yayi kisa sanadiyar kuskuren shi?
- Shin gaskiya ne kudin takarda (kamar NGN, £,€,$) ba zakka?
- Shin macen da aka saketa saki da ake kome, idan ta yi wani aure, har ta tare sannan sabon mijinta ya saketa, daganan sai ta koma gidan tsohon mijinta- shin zata gina akan wancan igiyar auren ta na farko ko kuma zata sake sabon zubi ne?
- Shin ana fitar da zakka ma kudin bashi?
- Qarin bayani akan wanda ya haddace Qur’ani ya bari ya zube
- Wanda ya manta sallar isha, idan ya tashi ramawa bayan rana ta fito (lokacin da ya tuna) shin zai asirta karatu ne ko zai bayyana?
- Wanda yayi wutri farkon dare zai sake wata wutrin idan ya tashi yayi wasu salloli a qarshen dare?
- Ya hallata mutum ya dinga roqon Allah don ya dade a duniya, alhali dan adam ba zai qetare ajalinsa ba!
- Hukuncin a saye abu a ajiye har sai lokacin da yayi tsada?
- Ya hallata mutum yayi kiyo don ya sayar lokacin kirsimeti.
- Bayani akan hada jam’i biyu a massallaci dake da limami da mai kiran sallah ratibai!
Download
Leave a Reply