Tambayoyi da amsoshin dake ciki
- Hukuncin wanda ya taya ‘yar uwanshi duren kunu ma danta marar lafiya. Sannan bayan dura mishi kunu sai yaron ya rasu. (Daga minti 2 zuwa minti 3)
- Hukuncin qarasa fadin Muhammadu rasulluh a qarshen iqama, la’akari da hadisin da yake cewa marowaci shine wanda aka kiran sunan Annabi bai masa salati ba (Daga minti 3 zuwa minti 8)
- Qarin bayan akan ayar – واعبد ربك حتى يأتيك اليقين (Daga minti 8 zuwa minti 10)
- Hukuncin wanda yake bin bashi, ya zame kudin da yake bi bashi lokacin zakka (Daga minti 10 zuwa minti 11).
- Hukuncin cin naman dake amfani da qwayoyin hallita samar da naman shanu da raguna “laboratory meat” (Daga minti 11:57 zuwa minti 13)
- Mace mai takaba zata iya fita bayan kwana arbain? (Daga minti 13 zuwa minti 15)
- Musulmi zai iya amfana da kudin mahaifinshi wanda ba musulmi ta hanyar wassici? (Daga minti 15 zuwa minti 16)
- Hukuncin mijin da ya mari matar shi saboda sa’in-sa da ya shiga tsakaninsu (Daga minti 16 zuwa minti 17)
- Adadin da yazo na karanta ayatul qursiy da suratul Ikhalas, da Muawidhatain a lokacin adhkar din safiya (Cikin minti 17).
- Bayyana rashin cin karo tsakanin ayar da take cewa babu tilas a addini da kuma hukuncin haddin kisa da ake yi ma wanda yayi ridda (Daga minti 17 zuwa minti 22)
- Ya hallata mutum da yake sayan kayan gona ma wani, ya sanya ladan shi akai? (Daga minti 22 zuwa minti 23)
- Ya hallata mutum ya ware wata rana domin bada sadaka? (Daga minti 23 zuwa minti 24)
- Ya hallata mutum yace “ta ya Allah kiwo yafi Allah na nan” (Daga minti 24 zuwa minti 26)
- Hukuncin wanda ya manta tahiya a sallah (Cikin minti 26 )
- Banbacin hukunce -Hukunce tsakanin azumin farilla da azumin nafila (Daga minti 26 zuwa minti 29)
- Lokacin karbar addua- shine tsakanin kiran sallah da iqama ko iqama da kabbarar harama (cikin minti 29).
- Akwai laifi ga dan kasuwan da yake sayar da kayan da mutanen china suke masa a Nigeria ma ‘yan Nigeria batare da ya bayyana musu a Nigeria ake yi kayan godon kada su ki sayan kayan? (Daga minti 29 zuwa minti 31)
- Akwai ingantacce hadisi akan matsar qabari? (Daga minti 32 zuwa minti 33)
- Hukuncin wanda ya manta karatun Sura a cikin sallah (cikin minti 33)
- Menene gaskiyan ba a zagin Shaidan (Cikin minti 34)
- Menene sahihancin cewa baitul ma’amur yana daidai da saitin ka’aba. (Daga minti 34 zuwa minti 35)
- Shin hidimar mace ga mijinta wajibi ne (Daga minti 35 zuwa minti minti 38)
- Mai karanta littafin “Qawa’idi” ma wanda basu sani ba- yana karantar da su abinda ya sani ba dadi ba qari yana da laifi? (Cikin minti 38)
- Fassarar hadisin “ wanda ya ambaci Allah shi kadai, ya zub da hawaye” (Cikin minti 39)
- Shin hadisin “…kullu bidiatin dalala na Irbad bin Sariya (Radiyallahu anhu)bai inganta ba? (Daga minti 40 zuwa qarshe)
Download
Leave a Reply