Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu 28-December-2019

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Shimfida: Hukunce- Hukunce lokacin sanyi tare da sauqin addinin musulunciBudewa zuwa minti 22


Tambayoyin dake ciki:

 1. Hukuncin yin sallama ga mai tsibbu ko mai duba? Daga minti 22 -26
 2. Shin hadisin da ke cewa idan mace ta wuce gaban mai salla ta yanke masa sallarsa ya shafi kowacce mace? Daga minti 26-27
 3. Hukuncin wanda yayi tafiya kasuwanci batare da iyalan shi ba yana sallar qasaru. Cikin minti 27
 4. Shin dole in miji zai qara aure ya sa uwargida a sabon gida, amarya a tsohon gida? Daga minti 28-29
 5. Hukuncin sunan Allah “ Ar-rasheed” da sunan mutum Abdulrasheed! Daga minti 29-30
 6. Hukuncin yin sallah gaban liman ranar jum’a. Daga minti 30-32
 7. Shin mace da ta sha azumi saboda laluran ciki ko shayarwa tare da ciwon ulcer- yaya za ta rama azumin da ke kanta? Daga minti 32-34
 8. Wanda ya kashe wani ba da gangan ba sannan yana da rashin lafiyan da ba zai iya azumi ba- yaya zai yi? Daga minti 34-36
 9. Shawara da neman addua ga mai yawan fada da mijinta. Daga minti 36-40
 10. Yaya marar lafiyan da salloli suka kubuce masa saboda alluran da ke sa shi bacci zai rama sallolin da ke kan shi da kuma sallolin da yayi su yana gyangyadi saboda tasirin allurorin da aka masa? Daga minti 40-42
 11. Yaya hukuncin sallar jum’ar ‘yan agaji masu gyara sahu lokacin hudubar jum’a? Daga minti 42-44
 12. Shin idan mace da miji suna musanyen ayyukan da ya wajaba ko zai ingantta zamantakewar su- za su samu lada? Daga minti 44-45
 13. Akwai laifi ga mutumin da zai yi fushi in an taka dokar Allah, ko da ma abubuwan da mutane suka saba aikata su? Daga minti 45-46
 14. Dagaske ne Mala’iku basa son warin tafarnuwa? Cikin minti 46
 15. Cire takalmi a wajen sallar gawa sunna ne? Cikin minti 47
 16. Shin yaya matsayin mayar da macen da aka saketa, tayi tafiya kafin ta kammala idarta, sannan bata amsa kiran wakilin mijinta na ta zo a mai da ita gidanta? Daga minti 48- 49
 17. Yaya wanda ke rike da kudin wani zai yi da kudin mutumin da ya neme shi bai same shi ba-Cikin minti 49
 18. Shin adalci ne miji ya dinga koya ma daya matar shi mota, ya bar daya matar shi? Daga minti 49 zuwa qarshe

Download


One response to “Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu 28-December-2019”
 1. […] Archive Fatawowin Rahama 28-12-2019 Fatawowin Rahama 22-12-2019 Fatawowin Rahama 21-12-2019 Fatawowin Rahama 15-12-2019 […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories