GA SAKON MALAM SA'ADU ZUNGUR NA WAKA SAMA DA SHEKARA 50 AMMA KAMAR YAU YA GABATAR(Sheikh Isa Ali Pantami)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

“Matukar a arewa da karuwai,
yan daudu dasu da magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
Matukar yayan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai tanyonsu da dukiya.
Babu shakka yan kudu zasu hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
In ko yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
Malaman karya yan damfara.
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
Wagga al’umma mai zata yo,
A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya sha kunya nan duniya “.
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko kuyi dariya.
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
waken sa mai suna “Arewa
Jamhuriya ko Mulukiya”.
O Allah forgive us and provide a
way out for us in this World and in
the next.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

11 responses to “GA SAKON MALAM SA'ADU ZUNGUR NA WAKA SAMA DA SHEKARA 50 AMMA KAMAR YAU YA GABATAR(Sheikh Isa Ali Pantami)”
 1. suleman abdullahi Avatar
  suleman abdullahi

  manzon allah sallalahu alaihi wassalama ya ce. mafi alkhairin ku shine wanda ya kuyi alkurani kuma, kuyar da shi

 2. babayamani Avatar

  Reblogged this on babayamani's Blog.

 3. Dini Avatar
  Dini

  الله أكبر

 4. Dini Avatar
  Dini

  الله أكبر كبيرا

 5. Isa Avatar
  Isa

  Food for thought

 6. Alhaji shehu Avatar
  Alhaji shehu

  Nawa ya Dade Yaya dadau!

 7. motar kara Avatar
  motar kara

  gaskiya dokin karfe ko kana ka kama ka hau

 8. Usman Idris Avatar

  thank God we have people like Isa pantami

 9. Adamu garba zungur Avatar

  Allah akbar kabiran

 10. Jamil Avatar

  I luv it!

 11. zaharaddin kabir Avatar
  zaharaddin kabir

  ameen Allah yaji kan maza

Leave a Reply

Latest updates
Categories