Hadith: Musulmi shine wanda Musulmai suka kuɓuta daga Sharrin Harshensa da Hannunsa

·

·

,

Imamul Bukhari da Muslim sun rawaito Hadisi daga Abdullahi Bin Amru yace: Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

المُسْلِمُ مَن سَلِمَ المُسْلِمُونَ مِن لِسَانِهِ ويَدِهِ، والمُهَاجِرُ مَن هَجَرَ ما نَهَى اللَّهُ عنْه

Sahihul Bukhari: 10. Sahihu Muslim: 40

Fassara/Sharhi

Cikakken Musulmi shine wanda ƴan uwansa Musulmi suka kuɓuta daga Sharrin harshensa da hannunsa. Mai Hijira na gaske shine wanda ya ƙaurace wa Abinda Allah ya hana.

Wannan Hadisi ne mai girma sosai wanda Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yake koyar damu Ladabi da

kuma halaye na Musulunci, wacce take ƙara

Haɗin kai da son Juna tsaƙanin Musulmai.

Wannan Hadisi yana nuna mana cewa cikakken Musulmi shine wanda baya cutar da ƴan uwansa Musulmi da bakinsa ko da hanunsa. Baya yi musu ƙarya, baya gulman su, baya zaginsu. Hakanan baya dukansu da hannunsa, ko ya sace musu kaya ko ya kashe su da sauran cutar wa da akeyi da hannu. Wannan cutarwa da harshe da hannu ya shafi wa’inda suke raye da matattu.

Idan mutum naso ya zamto cikakken Musulmi to dole sai ya ƙaurace wa Cutar da ƴan uwansa Musulmi da wa’inda ma ba Musulmi ba.

Hakanan yayi bayani cewa Cikakken mai Hijira shine wanda ya ƙaurace ya guje wa Abinda Allah Ya Hana.

Allah ya sanya mu cikin Musulmi na Gaskiya.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: