Mai Rubutu: Hamza Diso
Allah madaukakin sarki
Hanyar sanin Allah subhanu wa ta’alaa itace wahayin da Allah ya saukar wa bayinsa ta hanyar Annabawa.
Idan ka kalli Alkur’ani zaka ga gaba dayan sa yana magana ne akan Allah da abinda yake da alaka dashi, don kodai kaga magana akan sunaye da siffofin Allah ko kuma umarnin Allah ko hanin sa, sai kuma abinda Allah ya tanadarwa masoyan sa masu yi masa biyayya, ko ukubar da ya tanadarwa makiyan Addinin sa masu sabawa umarnin sa, ko ya bada misali akan wadanda sukayi masa da’a da yadda ya taimake so ko makiyansa da yadda ya halakar dasu ko yayi masu talala mai kamar sake.
Abin nufi dai shine:
Alkur’ani gaba dayan sa yana koyar da yadda za a san Allah da yadda za a sami yardarsa a kuma gujewa fushin sa don a sami kyakykyawar rayuwa a duniya da lahira.
Leave a Reply