Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Waswasi yana daga cikin abubuwa masu matuƙar tada hankali ga wanda Allah ya jarrabe shi dashi, wannan waswasin ya shafi mai girma ne ko ƙarami, misalin mai girma shine wanda zai rinƙa zuwa wa mutum yana sanya masa shakka a addinin sa. Misalin ƙarami kuma shine wanda zai rinƙa zuwa wa mutum yayin ibadar sa, kamar mutum yayi alwala sai ya rinƙa kokwanto kamar akwalar ta karye, ko kuma wani sauran fitsari ya fita masa, ko kuma yana sallah ya rinƙa tunanin Wani abu na duniya har ya mance raka’oi nawa yayi ko ya zamto hankalin sa baki ɗaya ya fice daga Sallar.
Duka wa’innan nau’uka na waswasi suna jefa Mutum cikin ƙunci, sai dai Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam bai barmu haka ba sai da ya nuna mana hanyoyin magance wa’innan nau’uka na waswasi.
Na farko: neman taimakon Allah da yawaita Addu’a da Zikiri: Shaiɗan ne yake kawo wa mutum waswasi acikin lamuran sa, idan mutum ya lazimci ambaton Allah da Addu’a to Allah maɗaukakin sarki zai magance masa wannan waswasi.
Kamar yadda aka rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi a gare shi yace;
Shaiɗan yana zuwa wa ɗaya daga cikin ku yace masa waye ya halicci kaza da kaza, har yace masa wanene ya halicci Allah, idan har mutum ya kai ga haka to ya nemi tsarin Allah sannan ya yanke waswasin
Sahih Muslim: 134
Haka nan Allah maɗaukakin sarki yace:
Kuma idan wata fizga daga shaiɗan ta fizge ka to ka nemi tsarin Allah.
Al-Araf: 200
Wannan Hadisi da aya suna nuna cewa Shaiɗan ne yake sanya wa mutum waswasi acikin lamuransa, kuma hanya da zaibi wurin kawar da wannan waswasi shine neman gudunmawar Allah. Yace “Auzu Billahi Minash-shaiɗanir-rajim”
Idan mutum yayi haka to Allah zai tsare shi.
Na biyu: mutum yayi iya ƙoƙari wurin tunkuɗe wannan waswasi kada yayi aiki da shi: idan waswasi yazo maka kayi iya ƙoƙari wurin tunkuɗe shi, Kada ka rinƙa amfani da wannan waswasi. Misali ka kammala alwala sai kaji kamar alwalar ka ta karye. To kada ka sake wata alwala har sai ka samu yaƙini cewa alwalar ta karye, da haka ne zaka tarbiyyantar da kanka wurin tunkuɗe waswasi.
Wani Sahabi ya kai koke zuwa ga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Mutum ne yake jin kamar alwalar sa ta karye acikin Sallah yaya zaiyi? Sai Annabi yace masa kada ya fice daga Sallar har sai yaji sauti ko yaji wari
Sahihul Bukhari: 137
Wannan Hadisi yana nuna Shakka baya kawar da yaƙini. Saboda haka koda mutum ya samu waswasi to kada ya karkata zuwa ga Wannan waswasin, yayi amfani da yaƙini da yake dashi.
Idan kuma waswasin da mutum yake fama dashi acikin Sallah ne kawai to ga yadda zaiyi.
An rawaito daga Usman bin Abil As Allah ya ƙara masa yarda yaje wurin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace masa
Shaiɗan ya shiga tsaƙani na da Sallah ta, da kuma karatu na(yana sanya min waswasi) yana rikitar dani, sai Annabi yace masa wannan wani shaiɗani ne da ake kiransa “khanzab” idan kaji shi(wannan waswasin) to ka nemi tsarin Allah daga gare shi, sannan kayi tofi a gefen hagun ka sau uku, sai yace na aikata sai Allah ya tafiyar min da wannan waswasin
Sahih Muslim: 2203
Idan ya zamto mutum na Sallah waswasi na damun sa to zaiyi isti’aza(Auzubillahi minash-Shaiɗanir-Rajim) sannan yayi tofi a gefen sa na hagu sau uku.
A taƙaice: Maganin waswasi shine yawan ambaton Allah da addu’a da neman gudunmawar Allah kan tunkuɗe shi, haka nan kuma mutum yayi iya ƙoƙarin sa wurin tunƙuɗe wannan waswasin kada ya bari yayi masa tasiri. Da wa’innan hanyoyi insha Allah mutum zai rabu da waswasi ko ya rage shi.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply