Hukuncin Jalasatul istiraha a Sallah

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: Menene Jalasatul Istiraha da kuma hukuncin ta

Amsa: Jalasatul istiraha shine zama da mutum zaiyi bayan ya ɗago daga sujada ta biyu kafin ya miƙe tsaye a raka’a ta farko da ta uku. sai ya ɗan zauna kaɗan sai yayi kabbara ya miƙe.

Menene Hukuncin sa? Wasu Maluma sun tafi kan cewa Jalasatul istiraha ba Sunnah bace idan har ba mutum yana da buƙatar yin ta bane. Misali bashi da lafiya ko girma ya kama shi.

Dalilansu: Mu’awiyah Bin Abi Sufyan ya rawaito Hadisi daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Kada ku rigani cikin Ruku’i ko sujada, domin Girma ya kamani nayi rauni

Abu dawud: 619. Ibn Maja: 797

Maluman da suke tafiya kan cewa Jalasatul istiraha ba Sunnah bace sukace Wannan yana nuna cewa Annabi bai fara Yin Jalasatul istiraha ba sai da girma ya kamashi. Jikin sa yayi rauni.

Haka nan sukace mafi yawancin Siffar Sallar Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da aka rawaito ba’a ambaci Jalasatul istiraha aciki ba. Da ta kasance Sunnah ce da duk wanda ya siffanta Sallar Annabi da ya ambace ta. Saboda haka ne za’a fahimci cewa Annabi yayi ne saboda buƙatar hakan.

Magana ta biyu: Wasu Maluman sun tafi kan cewa Jalasatul istiraha Sunnah ce kuma wannan magana itace tafi dace wa da daidai.

Dalilan su: An rawaito daga Malik bin Huwairith yace:

Ya ga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana Sallah, in yana Raka’a ta farko acikin Sallar sa to baya miƙe wa har sai ya daidaita a zaune

Bukhari: 823

An rawaito daga Abu Humaid ya siffanta Sallar Annabi yace:

Sannan ya tafi zuwa Sujjada, sannan ya shimfiɗa ƙafarsa ya zauna har sai ko wani gaɓa ya koma gurbin sa, sannan sai ya tashi

Abu dawud: 730. Attirmidhi: 304

Sannan Sukace abinda ya wakana acikin Sallah kuma aka rawaito shi to za’a lissafa shi cikin Sallah. Matuƙar ba ansamu dalili ne wanda zai nuna cewa anyishi ne saboda wani dalili ba.

Abin lura: Magana da tafi ƙarfi shine Jalasatul Istiraha Sunnah ce. Ba dole sai mutum ya tsufa ko bashi da lafiya ba yayi. Sai dai idan Limami da kake bi Sallah baya yi to rashin yin ka shine yafi domin kada ka tsaɓa wa limamin ka. Domin koyi da Liman wajibi ne, ita kuma Jalasatul Istiraha Sunnah ne. Saboda haka za’a ƙaddamar da bin liman kan Jalasatul Istiraha. Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates