Hukuncin shan ruwa a tsaye

Danna nan domin shiga karatu Online

Anas bin Malik ya rawito Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi tsawa game da shan abu a tsaye kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi 2024.

Wannan hadisi ne a bayyane da yake nuni kan hanin Mutum yasha abu a tsaye. Sai dai kuma an sake rawaito wani hadisin daga ibn Abbas cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yasha ruwan Zam Zam a tsaye. Kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta 5617.

Haka nan An rawaito daga Aliyu Bin Abi ɗalib an kawo masa ruwa yasha a tsaye sai yace:

Wasu mutane suna ƙin shan ruwa a tsaye, toh haƙiƙa naga Annabi ya aikata kamar yadda nima na aikata.

Sahihul Bukhari Hadith No: 5615

Wannan hadisai biyu da muka kawo a ƙarshe suke nuna halaccin shan ruwa a tsaye.

Imamun-Nawawy da Ibnul Qayyim sun Rajjaha cewa shan abin sha a tsaye Makruhi ne amma ba mai ƙarfi ba, Sabida haka ne ma Annabi yasha a tsaye sabida ya nuna halaccin sa in akwai buƙatar hakan.

Sabida haka: Shan ruwa a tsaye Ba haramun bane sai dai sha a zaune shine yafi dace wa kuma mutum yafi samun natsuwa, amma in mutum yasha a tsaye sabida buƙata toh babu laifi a hakan.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates