Hukuncin wanda fitsari ko Maziyyi ya fito masa yayin Sallah

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: Meye hukuncin Sallar mutumin da Maziyyi ko Fitsari ya fito masa yayin Sallah?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Idan Mutum yana Sallah sai yaji sauƙan wani abu, Fitsari ne ko maziyyi ne ba zai yanke Sallar sa ba sai ya tabbatar da Haƙiƙa wani abu ne ya fito. Domin sau da dama waswasin shaiɗan ne kawai, mutum zaiji kaman wani abu ya fito amma idan ya duba sai yaga babu komai.

An tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Mutumin da yake jin wani abu a Sallar sa, kamar alwalar sa ta karye, sai Annabi yace: kada ya fice daga Sallar har sai yaji sautin fitan wani abu, ko kuma yaji wari

Sahihul Bukhari: 137

Wannan Hadisi yana nuna cewa ba’a gina hukuncin warware war Alwala har sai an samu yaƙini.

Saboda Haka sai mutum ya tabbatar da cewa haƙiƙa Fitsarin ya fito masa, ko Maziyyi ya fito masa. Idan har ya tabbatar da Hakan ya auku to alwalar sa ta karye. Dole ya yanke Sallah yaje ya sake alwala, sannan ya tsarƙaƙe jikinsa ya sake Sallah.

Amma idan ya zamto cewa kowani lokaci hakan yana faruwa dashi, ma’ana yana fama da rashin lafiya da fitsari yana fita masa ba tare da niyya ba to anan hukuncinsa Hukuncin Mai Istihada(Jinin Ciwo) ne. Zai rinƙa yin alwala wa kowani Sallah, sannan ko yana cikin Sallah fitsari ya fito masa bazai yanke Sallar sa ba.

Hakanan Hukuncin wanda yake fama da sauƙar Maziyyi a kowani lokaci.

Amma idan bayan ya Kammala Sallah ne yaga Alaman Maziyyi ko fitsari ya fito masa Amma baisan yaushe ne ya fito masa ba to basai ya sake Sallar ba. Wannan Shine Fatawar Sheikh Bin Baz Allah yayi Masa Rahama.

Imamun-Nawawi Allah yayi masa Rahama yace:

Idan ya sallame daga Sallar sa, sannan sai yaga Najasa a jikinsa zai yiwu ya same ta kafin Sallah ko bayan Sallah, to Sallarsa ta inganta ba tare da Tsaɓani ba.

Almajmu’u: 3/163

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates