Meye hukuncin wanda ya mutu ana binshi bashin azumin Ramadana?
Wanda yasha azumin watan Ramadan da uzuri na rashin lafiya wanda wannan rashin lafiyar ana masa zaton zai warke, amma sai bai samu warke wa ba har Allah ya karɓi ransa toh babu komi akansa, kuma waliyyansa ba sai sun biya masa wannan azumi ba, sabida Hakkin Allah ne akansa, kuma baisamu daman sauƙe ta ba, kuma rashin sauƙetan ba dun sakaci bane.
Amma in ya zamto mutum yasha azumin Ramadan sabida rashin lafiya sai ya samu sauƙi da zai iya rama azumin da yasha sai bai rama ba har ya mutu toh akwai zantuka biyu na Maluma kan hukuncinsa
- Na farko: Waliyyansa zasu biya masa wannan azumi sabida hadisi da aka rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda Annabi yace: Wanda ya mutu kuma akwai azumi akansa toh Waliyyinsa zaiyi masa wannan azumin. Sahih Bukhari: 1952. Wannan umarni na Annabi ana ɗaukansa akan Mustahabbanci sabida wata rai bata ɗauka laifin wata rai.
- Na biyu: Za’a ciyar ne a madadin ko wani rana, Waliyyansa zasu ciyar da miskini.
Haka nan koda mace ce tasha azumi sabida lalura tasu ta mata sai ana kammala watan Ramadan ta rasu toh babu komi akanta sabida sakacin ba daga wurinta yake ba.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply