Tambaya: Shin ya Halatta ayi magana yayin Huɗubar Juma’a?
Amsa: Haramun ne ayi magana yayin Huɗubar Juma’a koda ko Umarni da kyakkyawa da hani da Mummuna ne, Wannan babu tsaɓani tsaƙanin Maluma akan Haramcin haka.
An rawaito daga abi Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace: Manzon Allh tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Idan kace wa ɗan uwanka yayi shiru ranar Juma’a, alhali Limami yana Huɗuba to Kayi lagawu(Yasasshen zance)
Sahihul Bukhari: 934. Sahihu Muslim: 851
Wannan hadisi ya nuna ƙarara cewa baya Halatta ayi magana, koda ko kaga wani ne yana surutu sai kace masa yayi shiru to kaima kayi laifi ballantana shi mai maganar.
Sabida haka kuskure ne babba Mutum ya rinƙa surutu ranar Juma’a Alhali Limami yana Huɗuba, ko ya rinka amsa waya.
Shin ya Halatta Limami yayi magana da Mutane yayin Huɗuba?
Ya halatta ga Limami yayi magana da Mahalarta wurin idan akwai Dalilin yin Hakan. Kamar yadda Aka rawaito wani balaraben ƙauye ya shigo ya sami Annabi yana huɗubar Juma’a Sai ya nemi Annabi ya roƙa Musu Allah sabida Fari da ake fama dashi, Annabi ya saurare shi kuma ya roƙi Allah, Allah ya sauƙo da ruwa.
Anas Bin Malik ya rawaito wannan Hadisi.
Sahihul Bukhari: 933. Sahihu Muslim: 897
Allaj yasa mudace.
Leave a Reply