Danganta ɗa zuwa ga Allah babban laifi ne wanda sammai suna gab da su tsattsage, ƙassai suna gab da su kekkece hakanan duwatsu suna gab da su rikito saboda an danganta ɗa zuwa ga Allah. Kamar yadda Allah ya faɗa acikin Suratu Maryam aya ta 90.
Mafi yawancin kiristoci suna da Aqidar cewa Annabi Isa ɗan Allah ne saboda haka lokacin da suke bikin kirismeti suna Ƙudurce cewa wannan biki da sukeyi suna yin sa ne domin murnar haihuwar ɗan Allah. Wannan kalma da suke furta wa ya girmama, ba komi suke faɗa ba face ƙarya.
Saboda haka lokacin da Musulmi yake taya su murnan kirismeti ya sani yana tsaɓa wa Allah ne, kuma kamar mutum ne ya aikata zina ko yayi kisan kai sai kazo kana taya shi murnan wannan mummunan aiki da ya aikata duk da cewa danganta ɗa ga Allah yafi girman lefi fiye da aikata zina.
Ya kamata Musulmi ya guje wa Taya kiristoci murnan kirismeti domin tsaɓon Allah ne.
Leave a Reply