Dan adam Allah yayi masa baiwa
da hankali da tunani sama da
sauran dabbobi, kuma aka
saukake masa hanyar kara kusaci
ga Allah, da fahimtar rayuwa ta
hanyar hore masa fahimta da
samun ilimi da aiki dashi.
Ilimi mai amfani shine ilimin Addini,
sai ilimin Rayuwa na sana’a, amma
ilimi mafi falala shine wadda ya
kara maka tsoron Allah, kuma aka
samu fahimtar addini a cikin sa.
Aiki da ilimi kuma shine amfanuwa
da abinda ka sani wajen bin
umarni, da nisantar abinda aka
hana ka, da himma wajen
kwadayin rahamar Allah da
nisantar dukkan hanyoyin halakar
da kayi. Hakanan cikin ilimin
sana’a da rayuwa mafi amfani
shine wadda ka aikata abinda ka
koya ka kware ta hanyar da aka
halatta maka.
Mu sani neman ilimi alama tsoron
Allah ne, kokarin neman karuwar
sa ibada ne, koyawa wani kamar
sadaka ne, yawaita bincike don a
kara fahimtar sa jihadi. Kuma mu
sani fa dukkan wahalar da ake sha
wajen tara ilimi, tsareshi kada a
manta, koyar dashi da aiki dashi
suke karawa rayuwa albarka da
samun yardar Allah a duniya da
lahira.
Illoli da matsalolin rashin ilimin
addini da rayuwa suna da yawa,
amma mafi hatsari shine suna
jawo asarar rayuwa da dauwama
cikin kunci, na duhun jahici dake
zama sanadin halaka duniya da
lahira. Hakika dukkan mu’amalar
da zakayi da maras ilimi ba zaka
gode ba, dubi yadda sakacin kin
neman ilimi ya jawo mana
kaskanci, da sabawa dokokin
Addini a dukkan rayuwar al’ummar
mu ta yau.
Yan uwa ku dubi yadda jahiltar
addini suka jawo mana tulin
matsaloli na mummunan
shugananci da kazamtaccen
jagoranci, ga lalacewar tarbiyya,
ga tulin aiyukan zunubi daga maza
da mata, yawan mutuwar aure,
gurbata kasuwanci, cin rashawa,
zaluntar juna, kin gaskiya cikin
magana da aiki, yaudara da
ha’intar juna, rashin tausayi da kin
taimakon juna, watsi da hakkokin
iyaye, da ‘ya ‘ya,ga kujewa aiyukan
lada, da nisantar yawan ibada.
Zukata sun cika da buri, harshe ya
zamo gabar zagi da surutu maras
amfani da karya, ba’a damuwa da
yadda ake tara dukiya ko batar da
ita, mutuwa ta zamo biki da bude
kofar lalata zumunta a rabon gado.
Kai saura kadan jahiltar addini ya
fara zama ajalin mu…! Yanzu mi
mukeyi ne da ba zamu koma ga
Allah mu nemi ilimi, muyi aiki dashi
ba don neman yardar Allah?
Wallahi duk wanda ya cuci
al’umma da ilimin sa, ko ya samu
ilimin yaki aiki dashi, ko ilimin ya
zamo abin alfahari da aikin riya, ko
yake halakar da al’umma don son
duniya to ya sani tabbas ya hala
kar da kansa, kuma duniya da
lahira bashi da rabo na alheri a
wajen Allah.
Leave a Reply