Emran Bin Hussein Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa:
Wanda ya karanta Al-qur’ani to ya roƙi Allah dashi, domin wasu Mutane zasu zo suna karanta Al-qur’ani suna roƙon mutane dashi.
Tirmidhi: 2917
Wannan hadisi yana nuna mahimmancin roƙon Allah da Karatun Alqur’ani, da kuma haramcin mutum ya karanta Al-qur’ani ya rinƙa roƙon mutane dashi, misalin masu zama a masallatai suna karatun Alkur’ani domin a basu sadaƙa, wannan baya halatta.
Ta yaya mutum zai roƙi Allah da Al-qur’ani?
Mutum zai roƙi Allah da Karatun Alqur’ani ne yayin karanta shi, ta yadda in mutum ya karanta ayah ta rahama sai ya nemi rahamar Allah, in ya karanta ayar Azaba ko wata fitina sai ya nemi tsarin Allah,
Haka nan kuma in ya kammala karatun zai iya tawassuli da wannan karatu da yayi domin roƙon Allah ya biya masa buƙatunsa. Hakanan mutum zai iya karanta Al-qur’ani domin neman samun natsuwa, domin da Ambaton Allah ne zuciya take samun natsuwa.
Leave a Reply