Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
Ka yarda da abinda Allah ya raba ya baka, zaka kasance mafi wadatan mutane.
At-tirmidi 2305
Rashin yarda da rabon Allah Yana daga cikin abubuwa masu janyo rashin kwanciyar hankali, da kuma rashin wadatar zuci ga ɗan Adam. Zaka ga mutum yana fama ta kowani hanƴa sai ya samu arziki, amma bai sani ba cewa komin ƙoƙarinsa da duk iya zafin nemansa bazai taɓa samun wani abu ba face abinda Allah ya raba ya bashi. Shi yasa annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake faɗa wa Al’ummarsa cewa:
ابن ماجه 2144
أيُّها النَّاسُ اتَّقوا اللَّهَ وأجملوا في الطَّلبِ فإنَّ نفسًا لن تموتَ حتَّى تستوفيَ رزقَها وإن أبطأَ عنْها فاتَّقوا اللَّهَ وأجملوا في الطَّلبِ خذوا ما حلَّ ودعوا ما حَرُمَ
Yaku mutane kuji tsoron Allah ku kyautata nema, domin babu wata rai da zata mutu sai ta sami duk abinda Allah ya Qaddara mata na arziƙi, koda ko ansamu jinkiri, kuji tsoron Allah ku kyautata nema. Ku ɗauki abinda ya halatta, ku bar abinda ya haramta.
A kullum mumini yana dogaro ne ga Allah, yayi riƙo da sababi, ya fita yaje neman arziƙi, yana da cikakken imani cewa wannan fita nema da yayi bashi zai kawo masa samu ba, sai dai Allah ne zai datar dashi ya samu, wannan fita da yayi, yayi ta ne domin bin umarnin Allah na yin riƙo da sabuba, kamar yadda mai jin yunwa zai ci abinci domin ya ƙoshi bazai zauna yace in Allah ya ƙaddara zan ƙoshi zan ƙoshi ba.
Allah yasa mudace, ya azurtamu da halal, ya karemu ga barin haram.
Leave a Reply