Malamai sunyi magana uku gamai
da kwanan Muzdalifah
1- Wajibine,daga wajibobin hajji
wanda ya barshi, sai yayi yanka,
maganar mafi yawan malamai
2- Kwanan Muzdalifah rukuni ne
daga rukunan hajji, hajji baya cika
sai da shi, raayin wasu malamai
biyar daga cikin tabi’ai,
3- Kwanan Muzdalifah, Sunnah ne,
kawai, inji Mal, Shafi’i
amma maganar da tafi rinjaye
maganar farko, ta masu cewa
wajibine,
MAGANA TA BIYU
hukuncin kwana ko rashin kwana a
Muzdalifah
1-Idan mutum Yayi Sallar Magariba
da Ishah, Yaci abinci zai iya
wucewa jifa a wannan daren basai
ya kwana ba
2- Idan Alhaji yakai rabin dare, zai
iya tafiya ba sai gari ya waye ba
3- Idan Alhaji yabar Muzdalifah
kafin alfijir ya keto sai yayi yanka,
don haka masu karfi baza su bar
Muzdalifah ba sai alfijir ya keto,
amma, mata da yara da raunana
suna iya tafiya daga Muzdalifah
bayan rabin dare domin su isa
wajan jifa da wuri,
Amma ya tabbata Annabi saw ya
kwana a Muzdalfah, mafi alkhairin
addini shine koyi da Annanbi saw.
Leave a Reply