MAN KUNTU MAULAAHU FA ALIYYUN MALAAHU

Danna nan domin shiga karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo



((من كنت مولاه فعلي مولاه))
(1). Yana daga cikin abin da ke ba wa mahankalta mamaki: Irin yadda ‘Yan Shi’ah ke gina addininsu a lokuta da dama a kan tsabar jahilci da son zuciya; daya daga cikin misalan hakan shi ne: Irin yadda su ‘Yan Shi’ah suka riki ranar goma sha takwas ga watan Zul Hijjah a matsayin Idin da ake samun lada ta hanyar yin bukukuwa a cikinsa; a cewarsu saboda a wannan rana ce Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi huduba a hanyarsa ta dawowa daga aikin hajjin bankwana zuwa gida Madina ya yi wani jawabi a wani guri da ake kira “Gadeer Khamm” ya ce a cikin jawabin nasa: ((Man kuntu maulaahu fa Aliyyun maulaahu)). Ma’anar wannan maga shi ne: “Duk wanda nakasance maulansa to Aliyyu ma maulansa ne”.
Sai ‘Yan Shi’ah suka nuna jahilci da son zuciya suka ce: da wannan lafazi da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi ke nan ya shaida wa Duniya ne cewa: da zarar ya mutu to Aliyyu Bin Abi Dalib ne khalifan Musulmai bayan mutuwarsa! Wannan shi ne jahilci da son zuciya da ‘Yan Shi’ah suka nuna; domin dukkan masana harshen Larabci, da kuma masana Alkur’ani da Sunnah suna sane da cewa: Ma’anar “Maulaa” a nan shi ne “Waliyyi” watau masoyi. Ma’anar wannan magana ta Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne: “Wanda duk na kasance masoyinsa ne to Aliyyu ma masoyinsa ne”.
Ga misalai daga Alkur’ani mai girma:-
1. Ayah ta 4 cikin Suratut Tahreem Allah Ya ce:-
{وان تظاهرا عليه فان الله هو مولاه وجبريل وصالح المؤمنين}.
Ma’ana: ((In kuka nemi taimakon juna domin kuntata masa, hakika Allah Shi maulansa (watau masoyinsa) da kuma Jibirilu, da saalihin Muminai)).
A nan babu wani mai hankali da zai ce: Mala’ikah Jibrilu da saalihin Muminai su ne shugabannin Annabi mai tsira da amincin Allah, a’a sai dai ya ce: su masoyansa ne.
2. Ayah ta 40 cikin suratul Anfal Allah Ya ce:-

{وان تولوا فاعلموا ان الله مولاكم فنعم المولى ونعم النصير}.
Ma’ana: ((Idan suka juya baya, to ku sani lalle Allah ne maulanku (masoyinku), kuma madallan Maulaa (Masoyi), kuma madallan Mataimaki)).
3. Ayah ta 78 cikin suratul Hajj Allah Ya ce:-
{واعتصموا بالله هو مولاكم فنعم المولى ونعم النصير}.
Ma’ana: ((Ku yi riko da Allah Shi ne Maulanku (masoyinku), kuma madallan Maulaa (Masoyin), kuma madallan Mataimakin)).
4. Ayah ta 11 cikin suratu Muhammad Allah Ya ce:-
{ذلك بان الله مولى الذين آمنوا وان الكافرين لا مولى لهم}.
Ma’ana: ((Saboda hakika Allah Shi ne Maulan (masoyin) wadannan da suka yi Imani, hakika Kafurai ba Maulaa (masoyi) gare su)).
5. Ayah ta 13 cikin suratul Hajj Allah Ya ce:-
{يدعو لمن ضره اقرب من نفعه لبءس المولى ولبءس العشير}.
Ma’ana: ((Yana kiran wanda cutawarsa ta fi zama kusa a kan anfanawarsa, tir din wannan Maulaa (masoyin), tir din wannan Abokin)).
6. Ayah ta 157 cikin suratul Baqrah Allah Ya ce:-
{الله ولي الذين آمنوا يخرجهم من الظلمات الى النور}.
Ma’ana: ((Allah masoyin wadannan da suka yi Imani ne yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske)). Ma’anar lafazin “Waliyyu” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
7. Ayah ta 55 cikin suratul Maa’idah Allah Ya ce:-
{إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم راكعون}.
Ma’ana: ((Abin sani dai shi ne: Allah da manzonSa da wadanda suka yi Imani watau wadannan da suke tsaida Salla kuma suke ba da Zakka suna masu rukuu’i su ne masoyanku)). Ma’anar lafazin “Waliyyu” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
8. Ayah ta 62 cikin suratu Yunus Allah Ya ce:-
{الا ان أولياء الله لا خوف عليهم ولا هم يحزنون}.
Ma’ana: ((Ku saurara lalle masu son Allah babu wani tsoro a kan su kuma ba sa yin bakin ciki)). Ma’anar lafazin “Auliyaa’u” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
9. Ayah ta 34 cikin suratul Anfal Allah Ya ce:-
{ان أولياؤه الا المتقون}.
Ma’ana: ((Babu masoya gare Shi sai masu taqawa)). Ma’anar lafazin “Auliyaa’u” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
10. Ayah ta 71 cikin Suratut Taubah Allah Ya ce:-
{والمؤمنون والمؤمنات بعضهم أولياء بعض}.
Ma’ana: ((Muminai maza da Muminai mata sashinsu masoya ne ga sashi)). Ma’anar lafazin “Auliyaa’u” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
11. Ayah ta 73 cikin suratul Anfal Allah ya ce:-
{والذين كفروا بعضهم أولياء بعض}.
Ma’ana: ((Wadannan da suka kafirta sashinsu masoya ne ga sashi)). Ma’anar lafazin “Auliyaa’u” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
12. Ayah ta 19 cikin suratul Jaathiyah Allah Ya ce:-
{وان الظالمين بعضهم أولياء بعض والله ولي المتقين}.
Ma’ana: ((Lalle Azzalumai sashinsu masoya ne ga sashi, Allah kuwa Masoyin Masu taqawa ne)). Ma’anar lafazin “Auliyaa’u” a nan shi ne ma’anar lafazin “Maulaa” a can.
Tabbas abin da wadannan nassoshi ke tabbatar wa al’ummar duniya shi ne:-
– Allah Madaukakin Sarki Masoyin Muminai ne, su ma Muminai masoyan Allah ne.
-Annabi mai tsira da amincin Allah masoyin Muminai ne, su ma Muminai masoya Annabi ne.
– Aliyyu Dan Abi Taalib Allah Ya kara masa yarda masoyin Muminai ne, su ma Muminai masoyan shi ne.
– Dukkan Muminai masoya ne ga yan’uwa su Muminai.
– Dukkan Kafurai masoya ne ga yan’uwa su Kafurai.
(2). Wani abu da ya kamata a ce ‘Yan Shi’ah sun fahimta shi ne: da dai ma’anar lafazin “Maulaa” shi ne ma’anar lafazin “Khilaafah”, haka nan da dai Annabi mai tsira da amincin Allah Khilaafanci da Khaliifa ne yake nufi to da sai ya ce: ((Man kuntu maulaahu, fa Aliyyun maulaahu ba’ada mautii)). Watau duk wanda nake shugabantarsa na mulki da Addini yanzu to Aliyyu shi ne Khalifahna bayan mutuwata!! To amma Annabi bai fadi haka ba, abin da kawai ya fada shi ne: ((Man kuntu mulaahu fa Aliyyun maulaahu)) kowa kuwa ya san cewa Sayyidina Ali ba khalifah ba ne a lokacin da Annabi yake raye, saboda babu yadda za a yi a samu Khalifah sai dai idan shi Annabi mai tsira da amincin Allah ba ya Duniya tukuna. Allah Ya taimake mu ya raba mu da sharrin Shaidan. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “MAN KUNTU MAULAAHU FA ALIYYUN MALAAHU”
  1. […] Source: MAN KUNTU MAULAAHU FA ALIYYUN MALAAHU […]

  2. SLM WANNAN HADISI RUWAYA DAGA SAHABBAY DARI DA ASHIRI DA TABI AY SAMA DA DARDI UKU

  3. Allah Ya Saka

Leave a Reply

Categories
Latest updates