Mas'alolin aure fitowa ta 16(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Domin neman ƙarin bayani danna nan

TAMBAYA;
Mene ne hukuncin zance?
AMSA
Lallai hadisai sun tabbata
wadanda a cikin su Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam yake
kwadaitar da mai neman aure ya je
ya ga wadda yake nema, domin
wannan shi zai janyo hankalinsa
zuwa son ta har ta kai shi ga auren
ta. Daga ciki akwai hadisin da Abu
Huraira radhiyallahu anhu ya ce:
ﻛﻨﺖ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻨﺒﻰ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺟﻞ ﻓﺄﺧﺒﺮﻩ
ﺃﻧﻪ ﺗﺰﻭﺝ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻣﻦ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ » ﺃﻧﻈﺮﺕ ﺇﻟﻴﻬﺎ « ﻗﺎﻝ ﻻ.
ﻗﺎﻝ » ﻓﺎﺫﻫﺐ ﻓﺎﻧﻈﺮ ﺇﻟﻴﻬﺎ ﻓﺈﻥ ﻓﻰ ﺃﻋﻴﻦ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﺷﻴﺌﺎ ».
Ma’ana:
Na kasance tare da Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam sai wani
mutum ya zo, ya ba shi labarin
cewa ya auri wata mace daga cikin
matan Madina. Sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam ya ce:
“Shin ka je ka gan ta?” sai ya ce:
‘A’a ban je ba.’ Sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam ya ce da
shi; Ka je ka gan ta, saboda akwai
wani abu a cikin idanun mutanen
Madina.
Haka kuma hadisi ya tabbata daga
Jabir Ibn Abdullahi radhiyallahu
anhu ya ce:
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ » ﺻﻞ ﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﺫﺍ ﺧﻄﺐ
ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻓﺈﻥ ﺍﺳﺘﻄﺎﻉ ﺃﻥ ﻳﻨﻈﺮ ﺇﻟﻰ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮﻩ
ﺇﻟﻰ ﻧﻜﺎﺣﻬﺎ ﻓﻠﻴﻔﻌﻞ ».
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam ya ce: duk wanda zai nemi
auren mace daga cikinku, idan ya
samu ikon ya kalli abin da zai ja
hankalinsa ga auren ta, to, ya
aikata.
A bisa wadannan dalilai wasu
malamai suke ganin cewa za a iya
kallon duk wani sashe na jikinta
wanda zai janyo hankalinsa ga
auren ta, amma ban da al`aurarta.
Wannan shi ne abin da Imamul
Auza’i ya fada. Sai dai mafi yawan
malamai suna ganin cewa, abin da
ya halatta a kalla kawai, shi ne
fuskarta da tafin hannunta, domin
su ne suke nuna kyawun mace.
Kuma sun shardanta cewa;
wannan kallon ya kasance don jan
hankali ne zuwa ga auren ta kawai,
ba don janyo fitina da tayar da
sha`awa ko faruwar fasikanci ba.
Haka kuma shari`ar Musulunci ta
hana mai neman aure kadaita da
wadda yake nema a zaure ko daki
ko falo ko kuma kadaita kowace
irin nau’i ce. Domin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam ya ce:
ﻻ ﻳﺨﻠﻮﻥ ﺭﺟﻞ ﺑﺎﻣﺮﺃﺓ ﻭﻻ ﺗﺴﺎﻓﺮ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺇﻻ ﻭﻣﻌﻬﺎ
ﺫﻭﻣﺤﺮﻡ…
Ma’ana:
Kada wani mutum ya kadaita da
wata mace, kuma kada wata mace
ta yi tafiya, face tare da ita akwai
muharraminta…
Mu sani cewa kadaita, tana jawo
fitina da waswasin shaidan. Don
haka, masu yin zance su yi hattara
da kadaita da matan da suke so.
Yana daga cikin mummunar
al`adar da ake aikatawa a wannan
zamani yadda ake yawaita zance
kullum da surutai marasa fa`ida.
Haka kuma yana daga cikin
dabi`un da ba su kamata ba, yi wa
mace alkawarin karya da nufin wai
za a cika mata bayan aure. Haka
kuma akwai masu yin aron sutura
ko abin hawa, yayin zuwa zance
don yaudara, duk wannan bai
kamata ba. Domin hadisi ya
tabbata daga Abu Huraira
radhiyallahu anhu ya ce: Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallam ya
ce:
ﺁﻳﺔ ﺍﻟﻤﻨﺎﻓﻖ ﺛﻼﺙ ﺇﺫﺍ ﺣﺪﺙ ﻛﺬﺏ ﻭﺇﺫﺍ ﻭﻋﺪ ﺃﺧﻠﻒ
ﻭﺇﺫﺍ ﺍﺅﺗﻤﻦ ﺧﺎﻥ
Ma’ana:
Alamomin munafiki guda uku ne!
Idan ya yi zance sai ya yi karya,
idan an ba shi amana sai ya yi
ha`inci, kuma idan ya yi alkawari
sai ya saba.
Saboda haka muna nasiha ga
`yan’uwanmu mazaje da su nisanci
wadannan siffofin marasa kyau.
Haka kuma su ma `yan’uwanmu
mata su ji tsoron Allah, domin babu
abin da ke sa a yi musu karya da
yaudara, sai kwadayi da son abin
duniya.
Haka kuma yana daga cikin
munanan al`adu a wannan zamani,
yadda wasu ke kwaikwayon
al`adun Turawa na yin hannu da
wadda suke so su aura, ko rike
hannunta da sauran abubuwan da
suke kai wa ga aikata alfasha da
fasikanci. Bayan kuwa hadisi ya
tabbata daga Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
…ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﻣﺴﺖ ﻳﺪﻩ ﻳﺪ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻗﻂ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺎﻳﻌﺔ ﻭﻣﺎ
ﺑﺎﻳﻌﻬﻦ ﺇﻻ ﺑﻘﻮﻟﻪ
Ma’ana:
… Na rantse da Allah! Hannun
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam bai taba shafar hannun
wata mace ba yayin mubaya’a, sai
dai yana mubaya’a da su ne ta
hanyar magana(ya ce na karbi
mubaya’ar ku).
Don haka idan har Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallam da Allah
ya aiko shi zuwa ga dukkan talikai,
kuma ya yi masa kariya daga
aikata sabo ya guji wannan, don
mene ne kai za ka fada cikin
wannan mummunan aiki alhali ba
ka da wani abin koyi fiye da
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam.
Haka kuma yana daga cikin
munanan dabi`u a wannan zamani,
ta yadda wasu masu neman aure
suke wassafawa abokansu kyawu
da kuma siffofin macen da suke so
su aura. Idan kuma ba sa son ta ko
kuma an samu sabani a
tsakaninsu, sai su rika aibata ta ga
mutane kuma su rika tona asirinta,
haka su ma matan suke aikatawa.
Kai! Abin ma har ya kai a
tsakaninsu suna aikawa juna
munanan sakwanni da hotuna na
batsa ta hanyar wasika a waya
(text message) da yanar gizo-gizo
(Internet), ta yadda za ka ga
`ya`yan musulmi suna aikawa da
hotunansu tsirara a shafin
Facebook da Twitter da 2go da
sauransu, Wa Iyazu Billah!
Wannan abu ya kai matukar muni
da lalacewar tarbiyya.
To, a nan muna so a fahimci cewa;
tushen mafi yawan matsalolin da
muka ambata, suna faruwa ne
daga iyaye, saboda sakacinsu ga
sha`anin tarbiyyar `ya`yansu
wanda yake kai su ga nadama
lokacin da nadamar ba za ta yi
amfani ba.
Nasiharmu ga `yan’uwa mata
kuma ita ce: su ji tsoron Allah, su
rike addininsu da mutuncin
gidajensu, kada don suna jin
wayewar kai, ko kiraye- kirayen
Turawan yamma na `yancin mata
ko zurfin ilimin zamani, ya sa mace
ta zubar da mutuncinta ko ta bayar
da kanta ga wanda ba mijinta ba.
Domin wannan zai kai ta ne kawai
zuwa ga halaka da hasara da
nadama a rayuwarta ta duniya da
lahira, lokacin da ba za su yi mata
amfani ba, saboda su ne aka fi
cutarwa da bata musu rayuwa
yayin da suka yi cikin shege ko
kuma mazan suka kyale su a
wulakance bayan sun gama da
su.Allah ya ganar da mu.

3 responses to “Mas'alolin aure fitowa ta 16(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. ADAMU NALOKO Avatar

    Amin. Jazakumul LAHU KHAIRAN

  2. Habibkn bigboy Avatar

    Allah yasa mudace

  3. zailani Alhassan Doguwa Avatar
    zailani Alhassan Doguwa

    Allah ya saka da alkhairi malamza

Leave a Reply to zailani Alhassan DoguwaCancel reply

Latest updates
Categories