ME YA FARU A KARBALA 13(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Yarima Ya Zama Sarki
Tun daga hudubar farko da Yazid
ya yi ya fara sauya siyasar mulki
daga ta babansa kamar yadda
hausawa suka ce, Sarki Goma
Zamani Goma. Yazid ya soma da
jajanta ma jama’a game da
mutuwar sarkin musulmi Muawiyah
a cikin hudubarsa, sannan ya bada
sanarwar biyan albashi na wata
uku a game (a wancan lokaci
talaka albashi gwamnati take yi
masa. Sunnar da sayyadi Umar
dan khattabi (R.A) ya fara). Sannan
Yazidu ya ce ya dakatar da yaki a
bangaren teku saboda gabatowar
lokacin sanyi. Daga juyayi sai
mutane suka koma murna.
Ba a birnin Sham kawai aka yi wa
Yazidu mubaya’a ba. A’a har da
Makka da Madina da Masar da
sauran garuruwan musulmi. Amma
mutane biyu da muka sani cewa ba
su yi mubaya’a ba tun wuri ayyana
Yarima suna nan a kan
matsayinsu. Kuma ganin kamar
gwamnan Madina Al-Walid bn
Utbah zai yi yunkurin tilasta su sai
suka sauya mazauni su biyun daga
Madina suka koma Makka.
Husaini (R.A) ya kwashe duk
iyalansa ya tafi da su in ban da
kanensa Muhammad bn Ali (Ibnul
Hanafiyyah) shi kam daman ya yi
mubaya’a kuma ya shawarci
wansa Husaini da ya canja ra’ayi
shi ma ya yi. Ya ce, shi bai ga
dalilin da musulmi zasu hadu a kan
wani mutum ba sannan a ki
amincewa da shi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates